James Ibori ya shiga uku

James Ibori ya shiga uku

– Tsohon Gwamnan Najeriya James Ibori zai bayyana a gaban Kotu a Kasar Birtaniya

– Watakila Ibori zai rasa makudan dukiyan sa

– An daure Tsohon Gwamnan ne dalilin laifin da aka kama sa da shi na cin hanci da rashawa a baya

James Ibori ya shiga uku
James Ibori ya shiga uku

Kwanan nan ne aka saki wani tsohon Gwamnan Jihar Delta James Ibori daga Gidan Yari a Kasar Birtaniya inda ya shafe shekaru kusan biyar bayan an same sa da laifin rashawa lokacin da yake Gwamna a Najeriya.

A karshen Watan jiya aka sako Gwamnan daga Gidan kaso inda ‘yanuwa da abokan arziki suka fito tarban sa. Sai dai da alamu har yanzu akwai matsala babba tare da James Ibori don kuwa ya gudu ne bai tsira ba.

KU KARANTA: Tashin hankali a Jami'ar Ilorin

Jaridar Cable ta rahoto cewa an sake komawa Kotu da James Ibori inda ya bayyana a gaban Alkali David Tomlinson na Kotun Southwark Crown. Watakila Ibori zai yafe makudan dukiyan sa wanda ya kusa Naira Biliyan 100 idan ba ayi wasa ba.

Dama can mun kawo labarin cewa a tsare Ibori a Gidan sa da ke Kasar Birtaniya bayan ya baro kurkuku. Sai dai Gwamnatin Najeriya za ta hada kai da Kasar Birtaniya wajen ganin an maido shi gida. Ibori ya handami sama da Dala Miliyan $250 na asusun Jihar Delta lokacin yana Gwamna.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Muna nan a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel