Abubuwa 13 da yakamata ku sani game da karin albashin malaman makaranta

Abubuwa 13 da yakamata ku sani game da karin albashin malaman makaranta

- Malaman makaranta a jiya Litinin sun samu manyan alkawurra daga shugaban kasa

- Ya bayyana cewa, ya gano malaman na fuskantar kalubale manya a fadin kasar nan

- Ya bayyana cewa, za a gyara musu albashinsu tare da yi musu wasu manyan gata

Malaman makaranta a Najeriya sun samu babban moriya ta ranar malamai ta duniya bayan shugaban kasa ya bayyana sabbin matakan inganta rayuwarsu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana sabbin tsari ga malaman da ya hada da karin albashi da kuma karin shekarun aiki tare da gina gidaje ga malaman.

Kamar yadda yace, malaman makaranta sun kasance tubali cigaban kowacce kasa da inganta tsaron ilimi. Malami ne ke gina rayuwar yara da kuma sanya su a turba

Shugaban kasar ya ce sanin halin da suke ciki da kalubalen da suke fuskanta ne yasa zai inganta rayuwarsu baki daya a kasar nan.

Ga abubuwa 13 da ya kamata a sani game da sabbin tsare-tsaren:

1. Karfafa guiwoyi tare da jawo hankulan masu digiri a kasar nan domin su rungumi malanta.

2. Gwamnati za ta kawo sabon tsari na bai wa daliban da ke karantun koyarwa a jami'o'i.

3. Samun aiki kai tsaye da zarar dalibi ya kammala karantar malunta a jami'a.

4. Asusun TETFUND a kasar nan zai dauka dawainiyar dukkan dalibai masu karatun koyawar a makarantun gaba da sakandare.

5. Za a fifita wadanda suka nuna hazaka a aikin koyarwa a kasar nan.

6. Za a saka sabon tsarin albashi na musamman ga malaman makarantun sakandare da firamare.

7. Za a dinga bai wa malaman kimiyya da na karkara alawus na musamman.

8. Gwamnati za ta samar da sabbin tsare-tsare na fansho ga malaman makaranta.

9. Gwamnati za ta kara yawan shekarun murabus zuwa 65 sannan shekarun koyarwa daga 35 zuwa 40.

10. Gwamnati za ta samar da tsari na musamman a koyarwa sannan za ta dinga bai wa malamai horo.

11. Malaman makaranta za su samu gidaje a birane wanda gwamnati za ta gina musu.

12. A kowacce shekara, gwamnati za ta dinga tsara yadda za ta bai wa malaman makaranta horo.

13. Gwamnatin za ta fadada lambar yabo ga malamai ta fannoni daban-daban.

KU KARANTA: Sabon hari: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 9, sun raunata wasu tare da sace wasu a Katsina

Abubuwa 13 da yakamata ku sani game da karin albashin malaman makaranta
Abubuwa 13 da yakamata ku sani game da karin albashin malaman makaranta. Hoto daga @BuhariSallau
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sama da shekaru 7 nake rufa wa matata asiri saboda darajar 'ya'ya - Fani Kayode

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sanda, M.A Adamu ya dakatar da ma'aikatan FSARS daga cigaba da ayyukansu, sakamakon korafin da 'yan Najeriya suke yi akan 'yan sanda na ta'addanci.

Ba su kadai wannan umarnin ya shafa ba, har da ma'aikatan STS, IRT da kuma ACS. An dakatar da ma'aikatan daga yin ayyuka kamar sintiri, tsayawa bincike, ba da hannu da sauran ayyukan da suke yi a kan tituna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel