Kudin Fansa: Masu Garkuwa Sun Yi Barazanar Hallaka Mutanen Abuja 11 da Aka Sace
- Kwanakin baya ‘yan bindiga suka shiga gidajen mutane a Abuja, aka dauke Bayin Allah da yawa
- Maganar da aka ji shi ne wadannan miyagu sun saki kadan daga cikinsu bayan miliyoyin kudi
- Sai dai, har yanzu akwai wadanda ba su fito ba domin ‘yan uwansu ba su iya tattaro kudi da babura ba
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ana cigaba da fuskantar barazanar rashin tsaro har a babban birnin tarayya na na Najeriya watau Abuja.
Daga cikin matsalolin da ake fama da su akwai ‘yan bindiga da ke garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
Miyagun da suka dauke mutane 18 a kauyen Kawu a karamar hukumar Bwari sun jefa al’umma a sabon dar-dar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust tace ‘yan bindigan sun yi barazanar kashe ragowar mutum 11 da ke hannunsu idan ba a biya masu bukata ba.
‘Yan bindigan sun fara barazanar ne saboda sun ce ana bata lokaci wajen biyan kudin karbar fansar da suka yanke.
An ba 'yan bindiga Naira miliyan 5
An bukaci dangin wadanda aka yi garkuwa da su, su biya miliyoyin kudi sannan su kawo sababbin babura kirar Bajaj.
A ranar Litinin da ta gabata, rahoton yace an saki mutane hudu, abin da ya cece su shi ne ‘yanuwansu sun biya kudi.
Sai da 'yan uwan suka lale Naira miliyan 5 kafin su iya ganin wadanda aka dauke.
'Yan bindiga sun sace mutane
Daga cikin wadanda aka dauke lokacin da aka shiga Kawu akwai wasu ma’urata, malamar asibiti da ‘ya ‘yan mai garin.
Wani ‘danuwan wadanda aka yi gaba da su, Bala Danjuma ya shaidawa jaridar sun yi waya da ‘yan bindigan da ke cikin jeji.
A cewar Bala Danjuma, idan mutane ba su hada kudi da kayan da ake bukata ba, za a dauki gawar ragowar wadanda ke tsare.
Wani mataki aka dauka Abuja?
An nemi jin ta bakin ‘yan sandan reshen Abuja game da lamarin amma kakakinsu, Adeh Josephine ba ta amsa sakon waya ba.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi alkawari zai magance matsalar garkuwa da mutane, ya kirkiri zama a kan batun tsaro.
Wike yana ganin akwai sakacin shugabannin kananan hukumomi a lamarin.
Asali: Legit.ng