Gyadar Dogo: Mutanen Da Suka Sha Da Kyar Da Aka Kifar Da Gwamnatin Najeriya a 1966

Gyadar Dogo: Mutanen Da Suka Sha Da Kyar Da Aka Kifar Da Gwamnatin Najeriya a 1966

  • A tsakiyar watan Junairu shekaru kusan 60 da suka wuce, sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula
  • Iyalan shugabannin lokacin da-dama sun kubuta duk da akwai wadanda suka gamu da ajalinsu a ranar
  • Ana tuna ranar nan ta shekarar 1966 a matsayin lokacin da yankin Arewa ya rasa manyan jagororinsa a tarihi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Da aka yi juyin mulki a farkon shekarar 1966, an rasa mutane da yawa daga cikin shugabanni zuwa jami’an tsaro.

Duk da kashe-kashen da aka yi, akwai wadanda suka tsira da kyar, Madaukakin Sarki SWT ya tsara da sauran kwana.

Juyin mulki
Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu yana Kano aka yi juyin mulki a 1966 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An rasa rayuka a juyin mulkin 1966

A juyin mulkin ne aka hallaka Samuel Ademulegun da matarsa wanda tarihi ya zo tana dauke da cikin wata tara lokacin.

Kara karanta wannan

Sunayen sojoji 10 da suka jagoranci kisa da kifar da mulkin Tafawa Balewa a 1966

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Chukwuma Nzeogwu Kaduna ya kashe Ahmadu Bello da matarsa da ta rungume sa, sannan ya kashe dogarinsa.

Baya ga Zarumi wanda yana cikin masu gadi, an kashe Ahmed B. Musa da Ahmed Pategi.

Rahoton nan ya tattaro sunayen daidaikun da suka sha a mummunan juyin-mulkin.

Su wanene suka tsira a juyin mulkin 1966?

1. Remilekun Adetokunboh Fani-Kayode

Mataimakin Firimiyan Kudu maso yamma, Remilekun Adetokunboh Fani-Kayode ya kubuta a yayin juyin mulkin na 1966.

Kamar yadda yaronsa watau Femi Fani-Kayode ya bada labari, Manjo Paul Tarfa da Kyaftin Takoda suka ceci ‘dan siyasar.

Sojojin tawayen sun tsare shi a barikin Dodan da ke Legas, sai wadannan jami’an tsaro suka kutsa, suka kubutar da shi a raye.

2. Sir Kashim Ibrahim

Na biyu kuma shi ne gwamnan tsohuwar jihar Kaduna Sir Kashim Ibrahim wanda sojojin da ke tare da gwamnati suka ceto shi.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasa da sojojin da aka kashe a juyin mulkin farko da aka yi a Junairun 1966

Wazirin Bornon ya zama ‘dan majalisa a 1951, daga baya ya yi ta rike mukamin minista kafin yin gwamna zuwa Junairun 1966.

Duk da ya tsira, bayan sojoji sun karbi mulki ya rasa kujerar gwamna, ya yi tsawon rai, bai rasu ba sai a 1990 yana mai shekara 80.

Akwai wadanda aka samu labari sojojin da suka shirya juyin mulkin sun yi garkuwa da su, amma daga baya an yi nasarar gano su.

Ta'adi a juyin mulkin 1966

Ana da labari a gaban iyalinsa aka dauke James Pam kuma Laftanan Kanal Arthur Unegbe ne kadai ‘dan kabilar Ibo da aka kashe.

Emmanuel Ifeajuna ya kashe Abubakar Tafawa Balewa, Zakari Maimalari da Abogo Largema a lokacin da aka nemi kifar da mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng