Babu Sauki: Darektan Yakin Neman Zaben APC Ya Bada Labarin Fadawarsa Hannun DSS

Babu Sauki: Darektan Yakin Neman Zaben APC Ya Bada Labarin Fadawarsa Hannun DSS

  • Femi Fani-Kayode ya iya zantawa da manema labarai bayan fitowa daga hannun jami’an DSS a Abuja
  • Darektan neman takaran Bola Tinubu ya ce bai fatan makiyinsa ya ji irin yadda ya ji da aka tsare shi
  • Fani-Kayode ya sha tambayoyi a kan zargin Atiku Abubakar da wasu sojoji da shirya juyin mulki

Abuja - Darektan harkokin sadarwa na zamani a kwamitin yakin neman zaben APC, Femi Fani-Kayode ya bada labarin shigarsa hannun jami’an DSS.

A ranar Litinin, jami’an tsaro masu fararen kaya suka zauna da Femi Fani-Kayode a dalilin ikirarin da ya yi cewa manyan sojoji su na shirin juyin mulki.

Daily Trust ta ce Cif Fani-Kayode ya shafe sa’o’i biyar yana amsa tambayoyi a hannun hukuma.

Bayan ya fito, ‘dan siyasar ya tattauna da ‘yan jarida a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Abuja, ya ce bai fatan ko da makiyinsa ya shiga halin da ya fada.

Kara karanta wannan

Zargin Darektan Yakin Zaben Bola Tinubu a 2023, Ya Jefa Shi a Hannun Dakarun DSS

Ba a taba tsohon Minista ba

Duk da haka, tsohon Ministan harkokin jirgin saman ya tabbatar da ma’aikatan da ya samu sun nuna kwarewarsu a wajen aiki, ya ce ba su taba shi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Fani-Kayode yake fadawa manema labarai cewa duk zaman nan da aka yi, ba a sallame shi ba tukun, zai sake komawa domin amsa wasu tambayoyi.

Fani-Kayode
Femi Fani-Kayode Hoto: @RealFFK
Asali: Twitter

Na yi awa 5 ina shan tambayoyi

“Na shafe tsawon kusan sa’o’i biyar. An taso ni a gaba da matsa; sun bincike ni da kyau, kuma sun nuna kwarewa sosai wajen bincikensu.
Sannan aka bukaci in sake dawowa ranar Laraba domin a cigaba da yin wasu binciken.
Ina tunanin babu inda mutum zai ji tsoron zuwa irin DSS. Da zan sake fadawa hannunsu a karo na biyu, ba zan rika bayani haka a Twitter ba.”

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Atiku Abubakar Ya Roki Jami’an Tsaro Su Cafke Tsohon Jigon PDP

- Femi Fani-Kayode

Vanguard ta rahoto Darektan yada labarai da wayar da kan jama’a na kwamitin yakin neman zaben APC, Bayo Onanuga yana cewa abin ya dame su.

Onanuga ya ce bayan samun labarin FFK yana hannun DSS, sun tuntubi Lauyoyinsu wadanda suka raka shi domin tabbatar da ba a keta masa hakki ba.

Da a ce an tsare shi har ya kwana, kwamitin kamfen ta ce da ta kalubalanci hukumar tsaron. Bayan fitowarsa, 'dan siyasar ya godewa jama'a a shafinsa.

Nasir El-Rufai ya tabo 'Cabals'

Ana haka sai aka ji labari Nasir El-Rufai yana cewa miyagun Fadar Shugaban kasa su na shirin hana ayi zabe, su na so a kafa gwamnatin rikon kwarya.

Gwamna Nasir El-Rufai ya ce wadannan mutane ba za su iya cin zabe ba domin ba su da nauyi a siyasa, sai dai su fake a bayan irinsu Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel