Sunayen Sojoji 10 da Suka Jagoranci Kisa da Kifar da Mulkin Tafawa Balewa a 1966

Sunayen Sojoji 10 da Suka Jagoranci Kisa da Kifar da Mulkin Tafawa Balewa a 1966

  • A ranar 15 ga Junairun 1966, wasu sojoji suka hambarar da gwamnatin Abubakar Tafawa-Balewa
  • Emmanuel Ifeajuna da Nzeogwu C. Kaduna suka jagoranci juyin mulkin a manyan garuruwan Najeriya
  • Sojojin sun kashe wasu da ke rike da mukamai, amma ba a cikinsu aka samu wanda ya karbi mulki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A karshen 1965, aka samu wasu sojojin kasa, suka fara kitsa yadda za su kifar da gwamnatin tarayya ta farar hula a Najeriya.

Sojojin nan wadanda kusan dukkansu Manjo ne sun yi nasarar kawo karshen mulkin Abubakar Balewa, amma ba su yi nasara ba.

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya a 1970s Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Juyin-mulkin 1966: Su wanene sojojin?

Legit Hausa ta kawo sunayen wadannan sojoji:

Kara karanta wannan

‘Zunuban’ Emefiele da yana Gwamnan Bankin CBN da suka jefa shi a matsala yau

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Emmanuel Ifeajuna

Kusan Manjo Emmanuel Ifeajuna ya jagoranci juyin mulkin, tsohon gwarzon ‘dan wasan ya kashe manyan sojoji da hannunsa a birnin Legas.

2. Nzeogwu C. Kaduna

Manjo Nzeogwu Chuwuma Kaduna ya shiga gidan Ahmadu Bello, shi ya bindige Sardauna, matarsa Hafsatu da wani mai gadi da yayi kokarin kare su.

3. Timothy Onwuatuegwu

Ana tunawa da Manjo Timothy Onwuatuegwu a kan yadda ya kashe Birgediya Samuel Ademulegun da matarsa Latifah mai dauke da tsohon ciki.

4. Chris Anuforo

Manjo Chris Anuforo ake zargi da kashe Festus Okotie-Eboh, Laftanan Kanal Kur Mohammed da Laftanan Kanal Arthur Unegbe a juyin mulkin.

5. Don Okafor

Wanda ya taimaka wajen cafke Abubakar Tafawa-Balewa shi ne Manjo Don Okafor, yana da kusanci da Firayim Minista, ya fito ne daga Kudu maso gabas.

6. Humphrey Chukwuka

Shi ma Manjo Humphrey Chukwuka yana da hannu a juyin mulkin, shi aka bukaci ya kashe James Pam, amma bai zubar da jinin kowa ba a rikicin.

Kara karanta wannan

Ibadan: Adadin mutanen da suka mutu yayin da wani abu ya fashe a babban birnin jihar PDP ya ƙaru

7. Adewale Ademoyega

Manjo Adewale Ademoyega yana cikin sojojin da suka yi juyin mulkin, amma bai kashe kowa ba, ya rubuta littafi a 1981 a kan abin da ya faru.

Sauran sojojin da ke da hannu a juyin mulkin 1966:

8. Ben Gbulie

Kyaftin Ben Gbulie ya shiga juyin mulkin 1966 kuma daga baya aka tsare shi tare da Victor Banjo, yana cikin sojojin Biyafara a yakin basasa.

9. Emmanuel Nwobosi

Kyaftin Emmanuel Nwobosi ya bada gudumuwa wajen hambarar da gwamnati. Daga baya ya zama hadimin Chukwumeka Ojukwu a Biyafara.

10. Ognu Oji

Wasu sun ce Kyaftin Ognu Oji yana cikin wadanda aka hada-kai da su domin a canza gwamnati, a karshe Janar Aguiyi Ironsi ya hau mulki.

Su wanenen aka kashe a juyin mulkin 1966?

Kun ji labari sojojin tawaye sun kashe manya da yawa musamman daga yankin Arewa.

Abubakar Tafawa-Balewa, Sardauna Ahmadu Bello da wasu mutae fiye 20 da aka rasa a juyin mulkin na 1966 wanda ya barka Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel