Tuna baya: Ranar da Sardauna ya cika a hannun Manjo Nzeogwu Kaduna

Tuna baya: Ranar da Sardauna ya cika a hannun Manjo Nzeogwu Kaduna

A rana irin ta yau da ke cika shekaru 52 da aka hallaka Shugabannin Najeriya da su ka hada da Marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello. Mun kawo labarin yadda abin ya wakana.

Manjo Nzeogwu Chukwuma Kaduna shi ne wanda asalin sa Inyamuri ne amma tashin Garin Kaduna ya jagoranci Rundunar sa su ka hallaka Firimiyan Arewa na lokacin watau Sir Ahmadu Bello a cikin dare. Kafin na an fadawa Sardauna abin da ake shirin yi amma ya ce sam ba zai tsere ba.

Tuna baya: Ranar da Sardauna ya cika a hannun Manjo Nzeogwu Kaduna
Wani hoton Gamji Maza Sardauna a lokacin rayuwar sa

Sojan da ya jagorani wannan shiri watau Manjo Kaduna ya shiga har gidan Sir Ahmadu Bello Sardauna ya kamo shi cikin iyalin sa inda bayan Sojojin da su ka shirya juyin mulki su neme sa sun rasa. A wajen kashe Marigayi Firimiya an yi rashin sa’a, an hada da wata mai dakin sa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya maidawa Tunde Bakare martani

Kamar yadda Manjo Kaduna ya bayyanawa manema labarai na BBC a wancan lokaci sun kashe masu gadin gidan akalla 3 da bindiga kafin su auka inda Marigayi Gamji yake buya. Wannan abu duk ya faru ne a Kaduna a lokacin watan azumin Ramadan bayan an sha ruwa.

A cewar wadanda su ka yi wannan aika-aika dai su na kokarin gyara kasar ne sai dai nufin su bai kai inda ya kai ba aka taka masu burki. Bayan Sardauna an kuma kashe wasu Shugabannin Kasar da Manyan Sojojin Yankin a daren na 15 ga Watan Junairun 1966.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng