“Ba Cikakken Namiji Bane, a Raba Auren Mu”, Mata Ta Nemi Kotu Ta Datse Aurenta Na Shekara 27

“Ba Cikakken Namiji Bane, a Raba Auren Mu”, Mata Ta Nemi Kotu Ta Datse Aurenta Na Shekara 27

  • A wata irin shari'a da ba kasafai aka saba gani ba, wata matar aure ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta na shekaru 27
  • Matar mai suna Sa'adatu Ayuba ta shaida wa kotun cewa mijinta Jalija ya daina biya mata bukata a kwanciyar aure
  • Haka zalika ta zargin mijin da ajiye wata budurwa daban a waje, zargin da Jalija ya karyata kuma ya ce aure ne ya kara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Wata matar aure mai suna Sa’adatu Ayuba, ta bukaci kotun yankin Dei-Dei da ta raba aurenta da mijinta, Jalija, mai shekaru 27, bisa zargin rashin tabuka komai a gado.

Wacce ta shigar da kara ta auri Jalija kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada a shekarar 1997 kuma ta samu ‘ya’ya biyar masu shekaru 25, 22, 14, tara da bakwai.

Kara karanta wannan

DJ Cuppy: Rashin miji da ɗa abu ne mai ciwo, in ji diyar attajirin Najeriya Femi Otedola

Matar aure na so kotu ta raba aurenta da mijinta
Mu leka kotu: Matar aure na so mijinta ya sake ta, ya daina gamsar da ita a gado. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sa'adatu ta nemi kotu ta raba aurenta da Jalija

Sa'adatu Ayuba ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tun shekara biyu da suka wuce ya canja mun gaba daya, ba na gane kansa saboda ya samu wata budurwar a waje
"Ba ya iya gamsar da ni a mu'amalar aure, na gaji da halin da ake ciki da kuma halinsa gaba daya, don haka ina son a raba auren domin a yi mun adalci."

Wanda ake karar ya karyata zargin matarsa

A martanin da ta mayar, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito, Jalija ya ce zargin da matarsa ta ke yi masa na cewa ya na da budurwa karya ne, kuma ya ce:

“Na auri wata matar ne daban kuma ina taka rawar gani a matsayina na namiji, matar da na aura tana da ’ya daya, mun yi aure a kauyensu.”

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama wani matashi saboda bankawa gidaje 4 wuta a Gombe, karin bayani sun fito

Ya kara da cewa ya kasance yana biya wa mai karar duk wata bukata da take nema a matsayin sa na namiji.

Hukuncin da Mai shari'a Malam Saminu Suleiman ya yanke

Sai dai mai shigar da karar, ta yi zargin cewa mijin nata ne ya ce matar da ake magana kanta budurwarsa ce.

Ta ce ba ta da labarin cewa mijinta ya auri matar, kamar yadda Platinum Post suka wallafa.

Alkalin kotun, Malam Saminu Suleiman ya baiwa ma’auratan mako guda su sasanta lamarin cikin ruwan sanyi sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 17 ga watan Janairu domin jin ta bakinsu.

Yan ta'adda sun datse hannuwan masunta a Borno

A wani labarin kuma, mayakan ISWAP sun datse hannun wasu masunta guda biyu a garin Marte, jihar Borno sakamakon kama su da laifin satar masu kifi.

Tun da farko dai, mayakan ne suka kwace kifin daga hannun masunta, amma saboda rashin wuri a kwalekwalensu, suka jefar da kwando biyu, su kuma masunta suka dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.