A shirye nake na biya Miji na sadakin da ya biya ni don ya sake ni – in ji wata mata

A shirye nake na biya Miji na sadakin da ya biya ni don ya sake ni – in ji wata mata

- Wani aure na barazanar mutuwa, kasancewar matar ta gaji

- Har ta yi tayin mayarwa da mijin sadakinsa don sa sake ta

- Amma alkalin kotun ya ba su 'yan kwanaki su sasanta kafin yanke hukunci

Wata mata mai suna Maimuna Jaafar ta kai karar mijinta mai shekaru 27 Abbas Kabiru kotu dake zamanta a Magajin gari bisa laifin rashin nema musu muhallin da zasu zauna ita da 'yarta 'yar shekaru 4 da haihuwa.

A shirye nake na biya Miji na sadakin da ya biya ni don ya sake ni – in ji wata mata
A shirye nake na biya Miji na sadakin da ya biya ni don ya sake ni – in ji wata mata
Asali: UGC

Kamar yadda kamfanin dillacin labarai ta kasa ya rawaito daga bakin lauyan mai karar Kabiru Alhassan, yace matar tana so a raba auren ne ta hanyar Khul'i.

Khul'i wata hanya ce da addini musulunci ya yarda da mace zata bukaci rabuwar aure ta hanyar maidawa mijin da ta ke aure sadakinsa.

Wakilin nata ya ce "Bata da bukatar cigaba da zama da shi a matsayin mijinya saboda tana gudun kar ta zama mace maras biyayya ga mijin nata, shi yasa ta yanke hukuncin maida masa da sadakinsa na Naira dubu 50,000.

Amma za ta rike kudin a matsayin wanda ta yi amfani da shi wajen ciyar da 'yarsu a tsawon lokacin da ba sa tare.

"Amma mai karar ta yanke hukuncin rike kudin sadakin a matsayin kudin shayarwa jaririnsu dan watanni shida da haihuwa.

Wanda ake karar yace sam bai san dalilin da yasa matar tasa take san rabuwar aurensu ba, amma shi tabbas yana son zama da matarsa, sai dai bai san me yasa ta shafe sama da shekara daya tana zaune a gidan iyayenta ba, bayan matsalar muhallai kadai gare su kuma shi ma tuni ya samu.

KU KARANTA: Cin amana: Wani saurayi ya ari kudin budurwarsa kuma ya auren wata daban ba tare da ta sani ba

"Tuni na samu gidan da zamu zauna, kuma na bayyanawa surukina halin da ake ciki, amma ban san me yasa har yanzu ba su neme ni ba, sannan kuma basu dawo da ita ba kuma a zahirin gaskiya bana son a rabani da matata da kuma 'yata", kamar yadda Kabiru ya bayyanawa kotu.

Bayan sauraron shari'ar, alkalin kotun Musa Sa'ad ya bayyana cewa tunda wadda take karar bata samu damar halartar kotun ba, ya ba wa mijin nata tsawon sati biyu domin yaje ya sasanta tsakaninsa da matarsa kafin su dawo a cigaba da sauraren shari'ar.

Ya dage zaman zuwa 18 ga watan Yulin da muke ciki domin sauraren labarin sulhu a tsakanin ma'auratan

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel