An Gano Sinadarin Benzene da Ke Cikin Man Fetur Na Iya Haifar da Cutar Sankarar Bargo

An Gano Sinadarin Benzene da Ke Cikin Man Fetur Na Iya Haifar da Cutar Sankarar Bargo

  • An yi kira ga jama'a da su kauracewa yawan tu'ammali da man fetur, barasa da sigari don kaucewa kamu da cutar sankarar bargo
  • A cewar Dokta Oladapo Aworanti na hukumar sarrafa jini ta kasa, masu yawan tu'ammali da magungunan kashe kwari na kamuwa da cutar
  • Bisa kididdigar hukumar lafiya ta duniya (WHO) da ta fitar a 2020, yawan 'yan Najeriya da suka mutu sanadin sankarar bargo ya haura 2,257

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Dokta Oladapo Aworanti, shugaban hukumar sarrafa jini ta kasa, shiyyar Kudu-maso-Yamma, ya ce wani sinadarin da cikin fetur na iya haifar da cutar sankarar bargo.

Cutar sankarar bargo ita ce ciwon daji na farin jini (kwayoyin da ke yaki da kamuwa da cuta) wanda ya samo asali daga bargon cikin kasusuwa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a wani babban kanti a jihar Nasarawa, sun kashe mutum 4

Abubuwan da ke haifar da cutar sankarar bargo
Cutar sankarar bargo ita ce ciwon daji na farin jini (kwayoyin da ke yaki da kamuwa da cuta). Hoto: Trustradio, Gettyimages
Asali: Getty Images

A cewar Dokta Aworanti, idan aka cire ciwon daji na mafitsara, kitse da hanta, sankarar bargo ce a gaba-gaba wajen saurin kama maza, kamar yadda ya zanta da jaridar Tribuneonline.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bisa kididdigar da WHO ta fitar a shekarar 2020, mutanen da suka mutu sanadin sankarar bargo a Najeriya sun kai 2,257.

Ta ya sankarar bargo ke kama mutane?

Kasancewar sankarar bargo na kama farin jini wanda ke yaki da cututtuka, to da zaran mutum ya kamu da cutar sankarar, jikinsa na iya kamu da wasu cututtukan cikin sauki.

Saboda kamuwa da cutar sankarar bargo, mutum zai rasa jan jini a jikinsa, daga nan zai fara jin wasu alamomi kamar suma da hajijiya, yawan gajiya, karancin numfashi, ciwon jiki da saurin bugun zuciya.

Menene ke kawo cutar sankarar bargo?

Har yanzu ba a san taka maimai abin da ke haifar da cutar sankarar bargo ba, kodayake cututtuka irin su 'Down's syndrome' da 'Fanconi anemia' na kawo cutar sankarar bargo.

Kara karanta wannan

Manyan shari'o'i 5 da aka gagara kai karshensu a shekarar 2023

Sauran abubuwan da ke haifar da cutar sun hada da hulda da sinadarai kamar benzene, wanda ake samu a cikin man fetur da magungunan kashe qwari, rahoton Mayo Clinic.

Ta ya za a gujewa kamuwa da cutar sankarar bargo?

Hanyoyin gujewa kamuwa da cutar sankarar bargo sun hada da rage yawan zuwa gwajin 'X-ray da CT scan' don gujewa 'radiation'.

Haka zalika, mutane su guji yawan amfani da magungunan kashe kwari, idan ya zama dole to a rinka amfani da makarin hanci, kuma a kaucewa sinadarai masu hadari.

Rahoto ya bayyana cewa yawan mu'amala da man fetur, barasa da sigari na haddasa cutar daji, ba wai mutuwar jan jini kawai ba, don haka a kaurace masu.

Hukumar Hisbah Kano ta kama mota makare da kwalaben barasa

A wani labarin, hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wata mota dauke da kwalaben giya dubu 24 a hanyar Kano-Zariya, tare da kama diraba da mutum biyu.

Daraktan hukumar, Alhaji Abba Sufi ya bayyana hakan a ranar Laraba a yayin da yake duba motar da aka kwace in da ya jinjina wa kokarin jami'an hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.