Tirkashi: Budurwa ta sha maganin kwari ta mutu, watanni uku bayan saurayinta ya kashe kanshi

Tirkashi: Budurwa ta sha maganin kwari ta mutu, watanni uku bayan saurayinta ya kashe kanshi

- Wata budurwa da ta shiga kuncin rayuwa ta sha maganin kwari ta mutu, watanni kalilan da saurayinta ya kashe kanshi

- An bayyana cewa budurwar ta aikata wannan aika-aika ne bayan zargin ta da dangin saurayin nata suke akan cewa sanadiyyar ta ne saurayinta ya kashe kanshi

- Mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa kawai ta dawo gida ne ta iske gawarta a yashe a kasa da yammacin ranar da lamarin ya faru

Wata budurwa da take koyon dinki a wani shago a jihar Legas, mai suna Adenike Fatai, ta kashe kanta watanni uku kacal bayan saurayinta mai suna Bayo Atanda ya kashe kanshi shima.

Budurwar mai shekara 25 wacce take 'yar asalin jihar Kwara wacce take zaune da mahaifiyarta a Igbekele, dake unguwar Shibiri cikin jihar Legas, an bayyana cewa ta shiga kuncin rayuwa tun bayan lokacin da saurayinta ya mutu, inda hakan yasa ta sha wani maganin kwari da ake kokwanton 'Sniper' ne.

Duk da dai ba ta bar wani rubutu ba lokacin da ta kashe kan natan, amma an duba shafinta na Facebook inda aka tarar da ta wallafa rubutu masu yawan gaske dake nuni da tana cikin kunci kuma za ta iya kashe kanta.

KU KARANTA: Me yayi zafi haka: Wata mata ta yiwa kanta saki uku ta hanyar tura sakon sakin ta wayar mijinta

Daga baya kuma an gano cewa wannan hali da ta shiga ya samo asali ne bayan zargin da dangin saurayinta suke yi mata na cewa ita ce ta jawo ya kashe kanshi.

Mahaifiyar budurwar mai suna Tawa, ta bayyanawa jaridar Punch cewa ta iske gawarta ne bayan ta dawo gida daga da yamma.

Tawa ta bayyana cewa Adenike ta shiga wani hali ne bayan mutuwar saurayinta, hakan yasa ta koma yankin Ikorodu da zama, ta kuma bayyana cewa za ta dawo gida idan ta samu saukin rayuwa.

Haka shima mahaifin budurwar mai suna Idris, ya bayyana cewa bai san cewa 'yar ta shi tana cikin wannan hali ba, ya ce shi kawai ya san yana yin magana da ita a waya ne tun bayan lokacin da suka rabu da mahaifiyarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel