Nazarin 2023: ‘Yan Siyasa, 'Yan takara da Fitattun Malamai 15 da Suka Mutu a Bana
Abuja - Shekarar nan ta zo da mutuwar manya-manyan mutane a duniya, hakan ya shafi sanannun mutane da ake da su a Najeriya.
Rahoton nan ya tattaro jerin sarakunan gargajiya, malaman addini, masu mulki da ‘yan siyasan da mutuwarsu ta girgiza kowa a 2023.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
1. Dr Chukwuemeka Ezeife
A shekarar nan aka rasa tsohon gwamnan jihar Anambra, Dr Chukwuemeka Ezeife wanda ya bar duniya yana shekara fiye da 80 da haihuwa.
2. Aisha Bello Mustapha
Mutane da-dama sun yi jimami da mutuwar ‘yar jaridar NTA, Aisha Bello Mustapha. Marigayiyar ta rike Manaja a tashar talabijin ta kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
3. Ben Nwabueze
Farfesa Ben Nwabueze SAN wanda fitaccen lauya ne ya rasu a Oktoban shekarar nan. Masanin shari’ar ya taba zama Sakatare na Ohanaeze Ndigbo.
4. Pa Akintola Williams
A bana ne babban Akantan farko a tarihin Najeriya, Pa Akintola Williams ya cika. Lokacin da Akintola Williams ya rasu, yana da shekaru 104 a duniya.
5. Mansur Bamalli
Magajin Garin Zazzau, Mansur Nuhu Bamalli yana cikin ‘ya ‘yan Zazzau da aka yi rashinsu a bana. Mansur Bamalli ya cika yana jakada a kasar Moroko.
6. Taiwo Akinkunmi
Har gobe za a rika tunawa da Pa Micheal Taiwo Akinkunmi domin shi ya zana tutar Najeriya, ko da ya rasu bayan jinya a Oktoba, ya kai 84.
7. Uchenna Ikonne
PDP ta rasa ‘dan takaranta na gwamna a zaben gwamnan jihar Abia a 2023. Farfesa Uchenna Ikonne ya rasu ne a sakamakon jinya a asibiti.
8. Aderonke Kale
A farkon Nuwamban shekarar 2023, Janar Aderonke Kale ta rasu. A kan tsohuwar sojar ne mace ta fara kai matsayin Manjo Janar a tarihin Najeriya.
9. Kayode Opelaye
Janar Opaleye Ekundayo Babakayode wani tsohon soja ne da ya cika a bana. Tsohon sojan ya yi gwamnan soja a jihar Ondo a shekarun baya.
10. Anthony Obi
Kanal Anthony Obi (mai ritaya) ya yi gwamnan soja a jihohin Abia da Osun. A jerin Legit, yana cikin shahararrun mutanen da aka yi rashinsu a 2023.
11. Ado Ibrahim
Mai martaba Sarkin Ebira, Ado Ibrahim ya yi sallama da duniya a shekara 94 a Oktoban bana. Sarkin ya rasu yana shekara 94 a wani asibiti a Abuja.
12. Yusuf Ali
Sheikh Yusuf Ali babban malamin addini ne da ya rasu a shekarar bana. Sarkin malaman na Gaya ya rasu ne a watan Nuwamban shekarar nan.
13. Mobolaji Ajose-Adeogun
Mutumin farko da ya yi Ministan harkokin Abuja a Najeriya shi ne Mobolaji Ajose-Adeogun. A tsakiyar bana ‘dan kasuwan ya rasu yana mai shekara 96.
14. Kamilu Ado Wudil
Hon. Kamilu Ado Wudil ya samu takarar ‘dan majalisar tarayya a NNPP ya rasu ana gabanin zaben 2023, daga baya yaron shi ya karbi tikitinsa a Kano.
15. Abubakar Giro Arungungu
Babban malamin musuluncin nan, Sheikh Abubakar Giro Arungungu ya rasu a 2023. Jama’a da-dama su ka halarci jana’izarsa da ake yi a jihar Kebbi.
Shugabar matan PDP ta rasu
Jam’iyyar PDP ta rasa shugabar mata ta kasa, Farfesa Stella Effah-Attoe a karshen shekarar nan. Marigayiyar ta na cikin fitattun mata a siyasa.
Stella Effah-Attoe ta zama shugabar mata ne bayan taron da aka yi a shekarar 2021.
Asali: Legit.ng