Babban Malamin Addinin Musulunci Sheikh Yusuf Ali Ya Rasu a Kano

Babban Malamin Addinin Musulunci Sheikh Yusuf Ali Ya Rasu a Kano

  • An yi rashin babban malamin addinin musuluncin nan Sheikh Yusuf Ali (Sarkin malamai Gaya) wanda ya rasu ranar Lahadi a birnin Kano
  • Babban malamin addinin musuluncin wanda ya rasu yana da shekara 73 a duniya, ya yi aiki a fannin shari'a lokacin da yake raye
  • Za a gudanar da jana'izar marigayin kamar yadda addinin musulunci ya tanada a gidansa da ke cikin ƙwaryar birnin Kano a ranar Litinin, 5 ga watan Nuwamba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Kano - Shahararren malamin addinin musuluncin nan na Kano Sheikh Yusuf Ali ya rasu.

Sheikh Yusuf Ali (Sarkin malaman Gaya) ya rasu yana da shekara 73 a duniya.

Sheikh Yusuf Ali ya rasu
Sheikh Yusuf Ali ya rasu yana da shekara 73 a duniy Hoto: Muslihu Yusuf Ali
Asali: Facebook

Ɗan siyasar nan kuma ɗa a wajen malamin, Muslihu Yusuf Ali, shi ne ya sanar da rasuwarsa ta shafinsa na Facebook a daren ranar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Babban ofishin Jakadancin ƙasar waje a Najeriya ya kama da wuta a Abuja, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanene Sheikh Yusuf Ali?

An haife shi a shekara ta 1950 a garin Gaya da ke jihar Kano, marigayin malamin addinin Musuluncin ya fara aikinsa a fannin shari'a a shekarar 1974 a kotun shari'ar musulunci a matsayin magatakarda, cewar rahoton Daily Nigerian.

Daga nan marigayin ya zama babban magatakarda, mataimakin rajistara, rajistara, alƙalin kotun babbar kotun shari'ar musulunci da darekta a babbar kotun shari'ar musulunci.

Ya yi ritaya a shekarar 2009 kuma ya cigaba da koyar da addinin Musulunci.

Za a yi jana'izarsa a gidansa da ke Unguwar Tudun Maliki cikin ƙwaryar birnin Kano da ƙarfe 1:30 na rana a yau Litinin, 6 ga watan Nuwamba.

Sheikh Ibrahim H. Musa ya riga mu gidan gaskiya

A wani rahoton, Sheikh Ibrahim H. Musa wanda aka fi da Albanin Kuri ya riga mu gidan gaskiya a gidansa da ke birnin Gombe na jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Makinde: Gwamnan PDP ya ciri tuta, ya yi ƙarin albashi mai tsoka ga ma'aikata da 'yan fansho

Malamin addinin musuluncin ya rasu ne bayan wasu ƴan ta'adda sun farmake shi tare da halaka shi a cikin gidansa.

Alƙalin Babbar Kotun Kwara Ya Rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa alƙalin babbar kotun jihar Kwara, Sikiru Adeyinka Oyinloye, ya rasu yana da shekara 58 a duniya.

Marigayi Alƙalin ya rasu ne ranar Lahadi, 23 ga watan Afrilu, 2023 bayan kwashe dogon lokaci yana fama da ciwon da ya shafi wuyansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel