‘Yan Majalisa Sun Nemi Kama Malamin Da Ya Soki Wadanda Sojoji Suka Kashe a Maulidi

‘Yan Majalisa Sun Nemi Kama Malamin Da Ya Soki Wadanda Sojoji Suka Kashe a Maulidi

  • Majalisar dokokin jihar Kano sun tattauna a game da kalaman da su ka fito daga bakin Baffa Hotoro a makon da ya wuce
  • Sojoji sun kashe mutane da-dama wajen maulidi a Kaduna, al’umma duk ta shiga jimamin wadanda aka kashe bisa kuskure
  • Amma an samu wasu malaman musuluncin da ke ganin mutuwa wajen taron maulidi ba kyakkyawan karshe ba ne

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta yi magana game da kalaman da aka ji sun fito daga bakin Sheikh Baffa Hotoro a makon jiya.

An ji Usman Abubakar Tasi'u Kiru a wani bidiyo yana bayani bayan Sheikh Baffa Hotoro ya soki wadanda aka kashe a Tudun Biri.

Kara karanta wannan

‘Yan APC sun fara harin matsayi tun da Ministan Tinubu ya hango kujerar Sanata

Baffa Hotoro
‘Yan Majalisar Kano sun bukaci a kama Baffa Hotoro Hoto: Amb Bashir Mohd Chokali
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da ake jimamin mutuwar mutane kimanin 100 a wajen maulidi, malamin addin ya yi wasu maganganu da suka jawo suka.

Majalisar Kano ta zauna a kan kalaman Baffa Hotoro

Hon. Usman Abubakar Tasi'u Kiru mai wakiltar mazabar Kiru a majalisar Kano ya gabatar da kudirin gaggawa a kan Baffa Hotoro.

Usman Abubakar Tasi'u Kiru wanda aka fi sani da Rabula ya zargi malamin da kalaman batanci, masu ban takaici da bakin ciki.

‘Dan majalisar yake cewa duk wanda ya ji kalaman Baffa Hotoro, zai fahimci akwai tunzura jama’a a ciki da zai iya jawo rikici a kasa.

Tudun Biri: An yi Allah-wadai da Baffa Hotoro

Yayin da ake makokin mutane 100 da jinyar wasu a asibiti, Hon. Usman Abubakar Tasiu ya ce kowa ya jajantawa mutanen Kaduna.

‘Dan majalisar yana ganin bai yiwuwa a sa’ilin da ake kukan wadanda aka rasa, a samu wani daga Kano yana munanan kalamai.

Kara karanta wannan

Sanusi ga ECOWAS: Ba a Sa Takunkumi ga Israila ba, Amma Kun Hana Nijar Abinci da Lantarki

Rabula ya ce Kano tayi fice wajen ilmin addini a Afrika, ya kuma nuna abin da Sheikh Hotoro ya fada ya saba da koyar musulunci.

Wani matakin gwamnati za ta dauka?

Ganin mugun tasirin abin da malamin addinin ya fada, 'dan majalisar na Kiru ya bukaci gwamnatin jihar Kano ta tuhume shi da laifi.

A ra’ayin ‘dan siyasar, sam bai dace a kamanta wadanda su ka rasu wajen zikiri da salatin Annabi Muhammad SAW da wasu fasikai ba.

Muhammadu Sanusi II ya yi fatan mutanen da su ka rasu sun yi shahada, akasin ra’ayin wasu malamai da ake zargi da zafin addini.

Bayan gabatar da kudirin, an yi zama na sirrin da a karshe ya kai ga yanke shawarar maganar ta je gaban Hisbah da majalsar shura.

'Yan majalisa sun taimakawa mutanen Tudun Biri

‘Yan Majalisar da su ka fito daga yankunan Arewa za su bada gudumuwar N350m kamar yadda aka ji domin a taimakawa Tudun Biri.

A sakamakon harin sojoji da ya kashe mutane wajen maulidi, Sanatoci sun hada masu fiye da N100m daga albashin da su ke karba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng