"Uwa da Ƴa Duk Cikin Ƙoshin Lafiya": Mata Mai Juna Biyu Ta Haihu Cikin Motar Bas, Bidiyon Ya Yaɗu
- Wata mata mai juna biyu ta haifi jariri a cikin wata motar bas ta kasuwanci da ta nufi garin Warri na jihar Delta
- Wata mata da ta yaɗa hoton bidiyo daga lokacin da aka haifa jaririn ta yi ƙarin haske kan yadda fasinjojin suka yi lokacin haihuwar
- Masu amfani da yanar gizo sun godewa Allah da ya ba wa jaririyar da mahaifiyarta lafiya yayin da suka yi mamakin faruwar lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Wata mata mai juna biyu ta haifi wata jariri a cikin motar kasuwanci da ta nufi garin Warri a jihar Delta.
Mai amfani da TikTok, @estacyc, ta sanya bidiyo kan yadda matar ta haihuwa a TikTok, inda ta yi nuni da cewa da mahaifiyar da abin da ta haifa duk suna raye cikin ƙoshin lafiya.
@estacyc taa ƙara da cewa matar ta haifi ɗiya mace kuma fasinjojin sun ji dadin wannan lamarin da ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Uwa da rai jariri da rai, fasinjoji suna murna." ALLAH YA YI, ƴar kyakkyawar yarinya.'' @estacyc ta rubuta a kan TikTok.
A cikin faifan bidiyon, wata mata a bayan fage ta bayyana cewa matar ta haifi jaririyar cikin sauƙi.
Ƴan soshiyal midiya sun taya ta murna
Babe ta rubuta:
"Omo barka da zuwa mummy V oo, nagode Allah ya bashi nasara, makwabciyata mai kirki."
user4269208030546 ya rubuta:
"Allah mun gode maka da ka sa muka samu daga cikin falalarka."
user5799821023267 ya rubuta:
"Idan namiji ne a sanya masa suna...Carlos idan kuma mace ce...a sanya mata suna Carlista."
Noney_Nwaeurop ta rubuta:
"Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki akan komai."
user8266375861487 ya rubuta:
"Allah ya baki lafiya."
Kyakkyawar Mata Ta Sauya Saboda Juna Biyu
A wani labarin kuma, wata kyakkyawar mata ta samu sauyin fasalin halittar ta lokacin da ta samu juna biyu wanda bai wuce watanni biyu ba da shigarsa a jikinta..
Gabadaya fasalin matar dai sun canja kamar ba ita ba duk kuwa da cewa juna biyun na ta ba wani daɗewa ya yi ba da samunsa.
Asali: Legit.ng