Kwamishinan Ganduje Zai Yi Shari’a da Angwaye da Amaren da Hisbah Ta Aurar a Kano

Kwamishinan Ganduje Zai Yi Shari’a da Angwaye da Amaren da Hisbah Ta Aurar a Kano

  • Wasu Angwaye da Amaren da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi wa auran gata a Kano sun yi karar Garba Yusuf a kotu
  • Malam Garba Yusuf ya fito ya na cewa an bada auren dubunnan mata a kan sadakin da bai isa a daura aure da shi ba
  • An yi karar tsohon Kwamishinan ne a gaban Abdu Abdullahi Wayya na Babbar Kotun Shari'ar Musulunci da ke Shahuci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Wasu daga cikin angwaye da amaren da aka aurar a karkashin tsarin hukumar Hisbah a jihar Kano sun yi karar Garba Yusuf.

A ranar Litinin, gidan rediyon Freedom ta fitar da rahoto cewa sababbin auren sun maka Malam Garba Yusuf a Babban kotun shari’a a Kano.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun koli: A karshe Tinubu ya maida martani ga kalaman Atiku Abubakar

Kotun musuluncin da ke Shahuci za ta saurari karar a karkashin jagorancin Mai Shari'a Abdu Abdullahi Wayya nan da kwanaki kadan.

Angwaye da Amaren da Hisbah
Daurin auren gata a Kano Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Auren gata: Za a shiga kotun shari'a a Nuwamba

Rahoton ya ce a an tsaida 6 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a fara shari’ar.

Garba Yusuf wanda ya rike kujerar kwamishina a Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ya soki auren gatan da gwamnatin Abba ta shirya.

Hisbah ta aurar da mata a kan N50, 000

A cewar Malam Yusuf, an aurar da matan ne a kan sadaki N50, 000 wanda hakan bai kai mafi akallan sadaki a zancen mazhabar Malikiyyah ba.

Akwai malaman da su ke ganin dole sai sadaki ya kai daya bisa hudu na dinari wanda a yanzu masana sun yi lissafin ya haura N53, 000.

Kara karanta wannan

Za a Biya Nnamdi Kanu Naira Biliyan 8 Bayan Kotu Ta Soke Haramcin Kungiyar IPOB

Angwaye da Amare sun garzaya kotu

Aminiya ta ce saboda ganin ya aibanta auren da aka yi masu, angwaye da amaren da su ka amfana da tsarin su ka shigar da kara gaban kotu.

Masu karar su na tuhumar tsohon Kwamishinan da yin kalamai na batanci a kafofin sada zumunta na zamani ga halataccen auren da aka daura.

A cewar wani ango da aka aurar a watan nan, abubuwan da Yusuf ya fada su na da tashin hankali, ganin cewa zai taba mutuncinsu a al’umma.

Haka zalika cewa idan an haifi yara ba ‘yan halal ba ne, zargi ne da zai shafi tsarkin iyali.

Wata Baiwar Allah ta ce saboda wannan cin mutunci ne su ka nemo kudi su ka kai kara a kotu domin a hukunta mai kokarin bata auren na su.

Malamai sun halarci auren gata a Kano

Ana da labari babban shehin Izala, Muhammad Sani Yahaya Jingir da wasu manyan jagorori sun je wajen walimar auren gata da aka yi a Jihar Kano.

Sakataren Izala na kasa, Muhammad Kabir Gombe ya samu zuwa bikin auren da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel