Karfin Hali: Labarin Wani Matashin Da Ya Dirkawa 'Yan Mata 3 'Yan Gida Daya Ciki

Karfin Hali: Labarin Wani Matashin Da Ya Dirkawa 'Yan Mata 3 'Yan Gida Daya Ciki

  • ‘Yan mata uku ‘yan gida daya sun samu ciki daga mutum mai gyaran lambu kuma bai da ko anini na kudi
  • An ruwaito cewa, ‘yan matan sun kasance a killace a gidansu, inda mahaifinsu ke boye su da kuma hana su fita ko ina
  • Lokacin da uwar yaran ta gano abin da ya faru, nan take ta sume, kana aka kori mai kula da lambun nan take

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani labari ya bayyana yadda wani mai kula da lambu ya samu ‘yan mata uku ‘yan gida daya ya banka musu ciki.

Tsohon sanatan Najeriya, Shehu Sani ya yada a Facebook cewa, ‘yan matan sun samu ciki ne duk da irin tsaro da killace su da iyayensu ke yi daga shiga mutane.

An tattaro cewa, talakan mai kula da lambun shi kadai ne aka ba damar ganin ‘yan matan da kuma kula su a rayuwarsu.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Ƙwararren Likita Yana Kan Aiki a Arewacin Najeriya

Kamar yadda yazo a rubutun da Sanata Sani ya yada, mai kula da lambun ya fara aikata lalata da ‘yan matan ne ba tare da sanin iyayensu da suka yi zurfi a addinin kirista ba.

Yadda matashi ya yiwa 'yan mata ciki
'Yan mata 3 da saurayin da ya yi musu | Hoto: ZED GOSSIP
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan samun labarin abin da ya faru, iyayen sun shiga mamakin yadda lamurra suka sauya duk da irin tsaron da suka sanya a gidansu.

A lokacin da aka tambaye su kan waye ya yi musu ciki, sai suka amsa da cewa mai kula da lambu ne, wanda hakan yasa mahaifiyarsu ta fadi a sume.

Yadda lamarin ya faro

Legit.ng ta gano cewa, mai kula da lambun ya fara kulla alakar zina da ta biyu cikin ‘ya’yan ne, wanda daga baya ‘yar fari ta gani abin da ke faruwa bayan kama su hannu dumu-dumu.

Domin neman ta rufa musu asiri, sai ‘yar farin ta nemi mai kula da lambun ya biya mata bukatarta kawai ita ma.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Hayakin Janareto Ya Yi Sanadin Rasuwar Ma'aurata, 'Yayansu Da Mutane 2 a Anambra

A lokacin da suke aikata alfasharsu, sai ta ukun ta shiga ta kama su hannu dumu-dumu suna aikata lalatar da ta kai ga daukar ciki, ita ma haka ta nemi a biya mata bukata.

Abin da suka aikata dai haka ya kai ga daukar ciki tsakanin ‘yan matan uku, wanda daga baya suka haifi ‘ya’ya.

Iyaye sun dauki kaddara

A bangaren iyayen, haka suka daddara suka dauki kaddarar da ta biyo kansu tare da ganin laifin kansu na killace ‘ya’yan nasu.

Duk da an kore shi daga aiki a gidan, har yanzu ‘yan matan na tura masa kudi kana suna kaunarsa a matsayin uban ‘ya’yansu.

Wani mawaki ya ce ya daina dirkawa mata ciki saboda wasu dalilai da ya bayyana a cikin rahotonmu na baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel