Yadda Wani Matashi Ke Ririta Ragonsa Wurin Ciyar Da Shi Biredi Da Shayi A Faifan Bidiyo

Yadda Wani Matashi Ke Ririta Ragonsa Wurin Ciyar Da Shi Biredi Da Shayi A Faifan Bidiyo

  • Bidiyon wani matashi ya girgiza Intanet bayan ganin yadda ya ke mu'amalantar ragonsa
  • Matashin na yi wa ragon wanka sannan ya wanke masa baki kafin ba shi biredi da shayi
  • Mutane da dama sun yi mamakin yadda matashin ya saba da ragon da alakar da ke tsakaninsu

Wani matashi ya girgiza Intanet ganin yadda ya ke ririta ragonsa kaman dan Adam.

An wallafa faifan bidiyon da aka nuna yadda matashin ke mu'amalantar ragon cikin kauna.

Matashi ya girgiza jama'a inda ya ke ciyar da ragonsa da biredi da shayi
Yadda Wani Matashi Ke Ririta Ragonsa. Hoto: TikTok/@playboi2370.
Asali: TikTok

Meye matashin ke ciyar da ragon?

Matashin wanda aka bayyana da Play Boi ya nuna yadda ya ke kula da ragon da ba shi abinci iri-iri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A faifan bidiyon, an gano yadda matashin ke wanke bakin ragon da buroshi kafin ciyar da shi, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Masani Ya Hasko Abubuwan Da Za Su Jawo Kayan Abinci Su Yi Masifar Tsada a Najeriya

Abin da yafi ba da mamaki shi ne yadda ragon ke cin biredi da kwankwadar shayi kamar yadda dan Adam ke yi.

Masu amfani da manhajar TikTok sun yi martani da mamakin yadda mutumin ya shaku da ragon.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Martanin mutane kan bidiyon da aka wallafa na matashi da ragon:

@ZT:

"Wannan ragon ya fi 'yan mata da yawa haduwa."

@tanty:

"Hatta dabbobi ma su na wanke bakinsu, amma mai gadi na ya ki ya goge na shi."

@Muhammad Umar:

"Dubi yadda ya ke ririta nama."

@I.J:

"Ko dai ragon budurwarka ne? Saboda ban gane komai ba."

@sonofsun:

"Ina fada muku wannan mutumin an ci amanarshi."

@CREED:

"Kai ace rago na cin abinci mai kyau."

@Cotede_Pablo03:

"Ka na ba shi biredi da shayi a bayyane amma a boye ka na ba shi bawon rogo."

Yadda juna biyu ya sauya fasalin wata mata, an yada bidiyon

Kara karanta wannan

“Ka Koma Gida Wajen Matarka” Budurwa Ta Fatattaki Magidanci Kamar Karamin Yaro, Ta Saki Hoton Hirarsu

A wani labarin, juna biyu ya jirkita fasalin wata mata tare da mayar da ita mummuna sabanin yadda a baya fasalinta ya ke.

A wani faifan bidiyo da aka yada a kafafen sadarwa an gano yadda halittar matar ya sauya saboda juna biyu da ta ke dauke da shi.

Abin da ya fi dauke hankalin mutane shi ne hancin matar da ya yi suntum fiye da a baya lokacin da ba ta da juna biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.