Hadimin Davido Ya Goge Sakon Neman Afuwa Da Ya Wallafa Yayin Da Mawaƙin Ya Yi Gum Da Bakinsa

Hadimin Davido Ya Goge Sakon Neman Afuwa Da Ya Wallafa Yayin Da Mawaƙin Ya Yi Gum Da Bakinsa

  • Hadimin Davido ya wallafa saƙon ban haƙuri a shafinsa na Instagram dangane da bidiyon da ake muhawara a kansa
  • Sai dai Israel Afeare, wanda ɗaya ne daga hadiman mawaƙin, ya goge saƙon ban haƙurin daga baya ba tare da bayyana dalili ba
  • Har yanzu dai Davido bai ce komai ba dangane da batun duk da neman ya fito ya nemi afuwa da mutane da dama suka yi masa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ɗaya daga cikin hadiman Davido, fitaccen mawaƙin nan na kudancin Najeriya mai suna Israel Afeare, ya goge wani saƙo na neman afuwar Musulmin Najeriya da ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta.

Israel ya ba da haƙurin ne saboda faifan bidiyon wata waƙa da mawaƙin ya ɗora a shafinsa na Twitter da ya janyo kakkausar suka daga Musulmin Najeriya kamar yadda ya zo a rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji Ta Bayyana Ainihin Dalilin Kama Sojan Da Ya Bar Musulunci Ya Koma Kiristanci

Hadimin Davido ya goge saƙon ban haƙurin da ya wallafa a shafinsa na Instagram
Hadimin Davido ya goge saƙon neman afuwan da ya wallafa a shafinsa na Instagram yayin da mai gidan nasa ya Gum da bakinsa. Hoto: Afeare Israel
Asali: Facebook

Bidiyon da ya janyowa Davido kakkausar suka daga Musulmin Najeriya

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne fitaccen mawaƙin David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido ya ɗora wani guntun bidiyo mai tsawon daƙiƙu 45 a shafinsa na Twitter.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin bidiyon an nuno mutane na sallah, sai kuma aka ga sun carke da rawa a bakin masallacin da suka gabatar da sallar.

Haka nan an hango ainihin mai waƙar, Logos Olori, wanda sabon mawaƙi ne kuma ɗaya daga cikin yaran mawaƙi Davido zaune saman masallacin yana waƙa.

Sai dai hakan bai yi wa mafi yawa daga Musulmin Najeriya daɗi ba, inda suka bi Davido da tofin Allah tsinen da ya sa shi goge bidiyon ba tare da ya shirya ba.

Israel Afeare ya goge rubutun da ya yi na ba da haƙuri

Kara karanta wannan

Bidiyon Matasa Na Kona Hoton Mawaki Davido a Maiduguri Ya Bayyana, Sun Nemi Ya Yi Abu 1 Rak

Daya daga cikin hadiman mawaƙin mai suna Israel Afeare, ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Instagram inda ya bai wa ɗaukacin al'ummar Musulmin Najeriya haƙuri kan bidiyon da mai gidansa ya wallafa da bai yi musu daɗi ba.

Ya ce mai gidan nasa ya ɗora bidiyon ne domin ya tallata yaronsa, wanda ya kasance sabon mawaƙi mai tasowa.

Ya ce Davido bai yi hakan da zummar cin mutunci ba, illah iyaka ya yi hakan ne domi nishaɗantarwa kamar yadda ya saba.

Sai dai hadimin mawaƙi ya goge rubutun daga baya, sannan kuma ba a ji mawaƙin ya ce wani abu ba har yanzu kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Matasa sun ƙona babban hoton mawaƙi Davido a Maiduguri

Legit.ng ta kawo muku wani rahoto inda aka ga wasu matasa a garin Maiduguri cikin wani bidiyo suna ƙonan babban hoton mawaƙi Davido.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Litar Man Fetur Za Ta Dawo Naira 50 Kacal a Najeriya, Fitaccen Malami Ya Faɗi Gaskiya

Matasan sun nemi Davido ya fito ya bai wa Musulmin Najeriya haƙuri dangane da batun bidiyon da ya janyo muhawara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng