Yar Birni A Kauye: Budurwa Ta Nuna Yadda Ta Ke Wanka A Bandakin Tabo Na Kauye A Karon Fari, Bidiyon Ya Yadu

Yar Birni A Kauye: Budurwa Ta Nuna Yadda Ta Ke Wanka A Bandakin Tabo Na Kauye A Karon Fari, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata budurwa da ta wallafa faifan bidiyonta ta na wanka a kauye ya jawo cece-kuce
  • Budurwar mai suna Florence, an gano ta a cikin bandakin tabo ko rufi babu ta na wanka
  • Mutane da dama sun mai da martani inda suke bayyana yadda muhallin kauyen ya burgesu

Wata budurwa 'yar birni da ta kai ziyara kauye ta nadi faifan bidiyon yadda ta yi wanka a bandakin tabo ko rufi babu.

Wadda ta wallafa bidiyon Florence ta ce ta ji dadin zama a kauyen shi ne ta yanke shawarar nadan faifan bidiyon don ma'abota shafin sada zumunta.

Bidiyon wata budurwa ta na wanka a bandakin tabo a kauye
Budurwa Ta Nuna Yadda Ta Ke Wanka A Bandakin Tabo. Hoto: TikTok/@florence355.
Asali: TikTok

Faifan bidiyon ya nuna yadda budurwar ke wanda a wani bandaki na tabo ko rufi babu, Legit.ng ta tattaro.

Saboda rashin rufi a bandakin ana iya ganin daga wuyanta har zuwa saman kanta yayin da ta ke wankan saboda rashin tsayin katangar bandakin.

Kara karanta wannan

"Ta Kwashe 'Ya'yana Ta Tafi Da Su": Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Da Suka Dade Ta Rabu Da Shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku kallin faifan bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu bayan ganin faifan bidiyon:

@soroti-Boyfriend:

"Yana yin tsarin gidan abin burgewa."

@hawa001:

"Kuma kafin ki je daki kura ya bule kafarki dole za ki sake kwara ruwa a kafar."

@wiz:

"Za ki iya neman tasi na Uber daga bandakin."

@user5571650107610:

"Rayuwar kauye kenan, muna iya magana da beraye har ma da sauro."

@Onthatile:

"Ina tsananin son irin wannan rayuwar."

@user80513795009028:

"Na kalli wannan faifan bidiyon ya fi sau biyar."

@Irene_A_Omanje:

"Haka na ke idan na koma kauye."

An Hangi Dan Shugaba Tinubu Da ‘Power Bank’ A Aljihunsa A Villa, Hoton Ya Jawo Mahawara

A wani labarin, Dan shugaban kasa, Bola Tinubu, Seyi Tinubu ya wallafa hotonsa a kafar sada zumunta.

Hoton ya jawo muhawara bayan da aka gano Seyi da waya a fadar shugaban kasa da kuma power bank a aljihunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel