Wasu Sabbin Ma'aurata Sun Shirya Bikinsu a Saukake, Hotunan Bikin Sun Janyo Cece-Kuce

Wasu Sabbin Ma'aurata Sun Shirya Bikinsu a Saukake, Hotunan Bikin Sun Janyo Cece-Kuce

  • Wani hoton wasu sabbin ma'aurata a Twitter da suka yi aurensu a sauƙaƙe ya janyo cece-kuce sosai a soshiyal midiya
  • Sabbin mata da mijin sun zaɓi hanya mai kyau wajen yin aurensu ba tare da sun takura kansu ba kamar yadda wasu ke yi
  • Ƴan soshiyal midiya sun yaba kan yadda suka yi aurensu, inda wasu suka yi ta yaba musu kan wannan gagarumar nasarar da suka samu

Wasu sabbin ma'aurata ƴan ƙasar Afrika ta Kudu sun zama abin magana a manhajar Twitter, bayan sun yi aurensu da ƴan kuɗaɗe marasa yawa.

Masoyan junan burinsu dai kawai shine su yi aure, wanda kuma sun samu cika wannan burin na yin auren.

Sabbin ma'aurata sun kashe kudi kadan wajen bikinsu
Hotunan bikinsu sun dauki hankulan mutane sosai Hoto: HermaineM
Asali: Twitter

Hotunan ɗaurin auren na su sun ɗauki hankula sosai. Inda masu amfani da Twitter suka bayyana aniyarsu ta kashe kuɗi ƴan kaɗan domin su shiga daga ciki.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Tayar Masa Da Hankali Lokacin Zabe

Rahotanni sun tabbatar da cewa ma'auratan sun biya R70 (N1680) ne kawai domin aurensu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hotunan bikin wanda @HermaineM ta sanya a Twitter ya nuna ma'auratan cike da farin ciki a ofishin yin rajistar aure bayan an ɗaura musu aurensu.

Ƴan soshiyal midiya sun bayyana ra'ayoyinsu

@Lomlom_27 ya rubuta:

"Ba wahalar da kai kan samo shinkafa da kajin da za a ba mutanen da daga baya za su je su yi ta gulma."

@QueenAtotwe ta rubuta:

"Irin auren da na ke so amma iyaye na ba za su bari ba."

@rap_sigma ya rubuta:

"Tabbas ɗan gajere kuma ƙayatacce, har kayanta sun yi kyau."

thabisomoyo__ ya rubuta:

"Bana son abinda zai sanya hankalin mutane ya karkata a kai na, aure zai sanya ni cikin ɗar-ɗar, ya fi kyau a ce kawai na je ofishin rajistar aure na yi abu na."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma Da Dama a Wani Mummunan Hari a Jihar Kaduna

@Shady_reign ya rubuta:

"Ba wai ina kushewa bane, na so a ce shi ma saki bai wuce R70 ba."

Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Na Neman Na Kanta Ya Dauki Hankula

A wani labarin na daban kuma, wata kyakkyawar budurwa ta tashi tsaye tana neman na kanta, inda ta buɗe wajen kasuwanci.

Budurwar ta yi wa kanta faɗa wajen yaƙi da zaman kashe wando, bidiyonta a wajen sana'arta ya ɗauki hankula sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel