Kyakkyawar Budurwa Ta Dukufa Neman Na Kanta, Mutane Da Dama Sun Jinjina Mata

Kyakkyawar Budurwa Ta Dukufa Neman Na Kanta, Mutane Da Dama Sun Jinjina Mata

  • Wata kyakkyawar budurwa ƴar Najeriya wacce ta buɗe wajen kasuwanci na gas, ta taya kanta murna a soshiyal midiya
  • Budurwar ta godewa Allah kan wannan nasarar da ta samu yayin da ta sanya bidiyon wajen kasuwancin na ta da aka yi shi da katako
  • Mutane da dama sun yaba mata inda suka bayyana cewa ta yi amfani kuɗaɗenta ta hanya mai kyau da ta dace

Wata kyakkyawar budurwa ƴar Najeriya ta yi wani ɗan gajeran bidiyo, wanda ya nuna sabon wajen kasuwancinta na wucin gadi da ta buɗe kwanan nan.

Wajen kasuwancin wanda aka yi shi da katakai, akwai tukunyar gas a ciki da abin gwaji, wanda ya nuna cewa za ta riƙa siyar da gas ne a wajen ga mutane masu buƙata.

Kyakkyawar budurwa ta kama sana'a
Mutane da dama sun yi mata murna Hoto: @midey_beauty_empire
Asali: TikTok

Budurwar mai suna (@midey_beauty_empire), ta taya kanta murna, inda ta bayyana cewa Allah ya yi mata gata sosai. Ta bayyana cewa lallai Allah ya shiga cikin lamuranta.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Gwamna Wike Ya Ba 'Yan Takarar Shugabancin Majalisa Muhimmiyar Shawara

Mutane da dama da suka yi tsokaci akan bidiyon sun bayyana cewa ta fi wasu da dama waɗanda har yanzu da iyayensu suka dogara domin samun kuɗin ɓatarwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

LegitHausa ta tattaro kaɗan daga ciki:

Hardey ya rubuta:

"Ina taya ki murna, babban rabo na nan tafe."

Educated_hypeman ya rubuta:

Kamfanin mai da gas na Kashamadupe."

Fadipe Eniola ta rubuta:

"Ina taya ki murna ƴanmata, Allah ya ƙaro buɗi sosai."

Ade_Asemota ya rubuta:

"Na taya ki murna.....wannan farawa ne, ke mai godiya ce. Allah ya albarkaci kasuwancin ki, ya sanya ya fi haka...amen

Falilat ta rubuta:

"Irin waɗannan ƴan ƙananan nasarorin abun a yi murna ne a kansu, musamman a halin da ake ciki yanzu a Najeriya da gari ya gayar da gari."

Budurwa Mai Tallar Kwai Ta Shirya Su Tsaf Kamar Bene a Farantin Talla

Kara karanta wannan

Jaruma Fati Muhammad Ta Hadu Da Sharrin Hatsabibin Boka, An Yi Mata Awon Gaba Da Muhimmiyar Kadara

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa mai tallar ƙwai ta zo da sabon salo wanda ya ɗauki hankulan mutane sosai.

Budurwar dai ta shirya ƙwayayen na ta akan farantin talla kamar wnai bene gwanin ban sha'awa. Mutane da dama sun cika da mamaki yadda ta iya shiryasu haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel