'Dan wasan kasar Amurka Zai Fita daga Duniya Domin Ya Shirya Wani Sabon Fim

'Dan wasan kasar Amurka Zai Fita daga Duniya Domin Ya Shirya Wani Sabon Fim

  • Tom Cruise yana shirin fita daga wannan Duniya da muke rayuwa domin ya shirya wasan kwaikwayo
  • ‘Dan wasan zai fito a wani fim da Doug Liman – mutumin da ya shirya The Bourne Identity, yake bada umarni
  • Idan Cruise ya samu yadda yake so, zai zama shi ne ‘dan farar hula na farko da ya taka kafa a wata Duniyar

United States - Shahararren ‘dan wasan kwaikwayo, Tom Cruise yana cigaba da bada mamaki bayan an ji yana shirin fita daga Duniya domin yin fim.

NYPost ta fitar da rahoto a makon nan cewa Tom Cruise mai shekara 60 a Duniya ya hada-kai da Darektan wasan kwaikwayon The Bourne Identity.

Cruise da Doug Liman za su hadu domin suyi wani fim wanda zai yi sanadiyyar da ‘dan wasan zai shiga kumbo, ya bar wannan Duniyar zuwa wajenta.

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyon Sojan Dake Satar Makamai Yana Kaiwa ‘Yan Bindiga Yayin da Dubunsa ta Cika

Shugaban kamfanin fina-finai na UFEG watau Donna Langley ya shaidawa BBC News cewa Tom Cruise zai kai su wajen Duniyar da mu ke rayuwa.

“Ina tunanin Tom Cruise zai kai mu wata Duniyar, zai kai mutanen Duniya zuwa wata Duniya.
Shirin da ake yi kenan. Muna da gagaruman shirin da muka yi tare da Tom (Cruise)…A dauki kumbo zuwa wajen Duniya domin ayi fim.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Donna Langley

Tom Cruise
Tom Cruise a shirin Edge of tomorrow Hoto: time.com
Asali: UGC

Jiran shekara 2 ya zo karshe

Tun a 2020 aka nemi ayi fim din, amma aka dakata saboda matsalar annobar COVID-19 a lokacin. Yanzu dama ta samu na karasa abin da aka yi niyya.

A wannan fim za ayi abin da ba taba ji ba, za a fita daga Duniyar da mutane suke rayuwa.

Kamar yadda jaridar gida ta Daily Trust ta kawo rahoto, Donna Langley yace za a shirya mafi yawan wasan kwaikwayon ne a wannan Duniyar ta mu.

Kara karanta wannan

Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

Idan ‘dan wasan ya yi nasarar cin ma wannan buri, zai zama mutumin farar hula na farko da ya yi yawo a wata Duniyar, kuma na farko a tarihin fina-finai.

Hakan na zuwa ne bayan tauraron ya fito a shirin Top Gun: Maverick wanda ya yi kasuwa. 'Dan wasan yana cikin taurarin da suka fi kware a Hollywood.

Damben Joshua v Usyk

A watan Agusta, an ji labari cewa a wasan damben da aka yi a Birnin Jeddah da ke kasar Saudi Arabia, Oleksandr Usyk ya sake doke Anthony Joshua.

Joshua wanda ‘Dan asalin Najeriya ne ya gagara karbe kambunsa daga hannun gwarzon WBA, IBF, WBO da kuma IBO a karawarsu ta biyu a jere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel