Ana ji Ana Gani, Fasinjoji Sun Babbake Kurmus da Mota Tayi Hadari a Kusa da Gada

Ana ji Ana Gani, Fasinjoji Sun Babbake Kurmus da Mota Tayi Hadari a Kusa da Gada

  • Wani mummunan hadari da aka yi a babban titi a Legas, ya yi sanadiyyar rasa mutane 12 nan-take
  • Hukumar LASEMA masu kula wajen bada taimakon gaggawa sun tabbatar da aukuwar lamarin
  • Motar Mazda KJA 699 GY ta kama ci da wuta ne a dalilin gangancin direba, wanda shi bai hallaka ba

Lagos Hukumar LASEMA masu kula wajen bada taimakon gaggawa a Legas, sun tabbatar da aukuwar wani mummunan hadari da aka yi a Legas.

A yammacin Lahadi, 25 ga watan Satumba 2022, Daily Trust ta rahoto cewa wata motar bas mai dauke da mutane 14 ta kama ci da wuta a kan hanya.

Jami’an hukumar LASEMA da suka isa wurin da abin ya faru, sun ce motar da ta kone, kirar Mazda ce mai lambar garin Ikeja a Legas, KJA 699 GY.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da bam ya tashi bayan sallar Juma'a, mutane da dama sun mutu

Hadarin ya auku ne a kusa da fitacciyar gadar nan wanda ake kira 3rd Mainland Bridge a Ikoyi. Premium Times ta fitar da wannan labarin a jiya.

Meya jawo hadarin?

Punch tace an yi hadarin ne a sanadiyyar tukin ganganci da sheka gudu da direban motar yake yi, hakan ya yi sanadiyyar da wuta ta rutsa fasinjoji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren din-din-din na hukumar LASEMA, Dr. Olufemi Oke-Osanyintolu yace direban ya kubuta, duk da shi ake zargi da sanadiyyar jarrabawar.

Gadar 3rd Mainland
Gadar Gadar 3rd Mainland Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Haka zalika an ceto wasu ‘yan mata uku, tuni aka wuce da su zuwa babban asibitin Gbagada. Da motar ta kama ci, wasu fasinjojin sun fice daga motar.

Kamar yadda Dr. Olufemi Oke-Osanyintolu ya bayyanawa manema labarai, jami’an LASEMA sun bada agajin gaggawa, sun iya ceto wani matashi daya.

Mutane bakwai sun rasu

Amma abin takaicin shi ne mata hudu da maza biyu da wani karamin yaro da ke cikin wannan mota duk sun kone, babu wani wanda yayi rai daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Najeriya Ta Shigesu: Farashin Danyen Man Ya Fadi A Kasuwar Duniya

Hukumar LASEMA tace ta tattara gawawwakin mutanen a motarsu, ta mika su zuwa asibiti.

The Nation ta kara da cewa shugaban LASEMA na jihar Legas yace jami’ansa za su karasa zuwa inda abin ya faru, domin dauke motar daga hanyar jama'a.

'Yan bindiga sun mutu

A makon da ya gabata, an samu rahoto Sojojin Najeriya sun shiga inda ‘yan bindiga suke, sun yi masu raga-raga a yankunan Katsina da kuma Zamfara.

Wata majiya ta fadawa manema labarai, a irin wadannan hare-hare ne ake zargin an bindige Dogo Rabe, wanda Kauyukan Zamfara sun san da zaman shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel