Alhamdulillahi: Uwargidar El-Rufai Ta Cika shekara 37, Babu Saki ko Yaji a Aure

Alhamdulillahi: Uwargidar El-Rufai Ta Cika shekara 37, Babu Saki ko Yaji a Aure

  • Hadiza Isma El-Rufai ta cika shekara 37 a Duniya tana tare da Nasir El-Rufai matsayin matar aure
  • Gwamnan na Kaduna a yau, Malam Nasir El-Rufai ya auri sahibarsa a shekarar 1985, har yau ana tare
  • Uwargidar jihar ta Kaduna ta bayyana cewa ba a taba samun ranar da tayi wa akalla El-Rufai yaji ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - A ranar Laraba, 17 ga watan Agusta 2022, aka ji Hadiza Isma El-Rufai tana mai murnar cikar ta shekara 37 da aure da Nasir El-Rufai.

A lokaci irin wannan a shekarar 1985, Malam Nasir El-Rufai ya auri sahibarsa, Hadiza Isma wanda ya ci karo da ita a jami’ar ABU Zaria

Tarihi ya nuna, kafin nan sun san junansu na kusan shekaru goma a Zaria, an daura masu aure a Kano, garin da aka haifi Hadiza Isma a 1960.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Ta Jero Jihohohin Arewa da za su yi Fama da Ambaliyar Ruwa

Kamar yadda Uwargidar Gwamnan ta taba bada labari a shafin Twitter, Malam El-Rufai ya farauci soyayyarta ne ta hanyar rubuta wasika.

Tun wancan lokaci ake caba soyayya tsakanin Malam El-Rufai da Hadiza Isma El-Rufai, yau tafiya tayi nisa har sun yi shekaru 37 da aure.

Da take magana a shafinta na Twitter dazu, Mai dakin tsohon Ministan tarayyar ta tabbatar da cewa ta shafe shekaru 37 a gidan auren ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hadiza El-Rufai
Uwargidar El-Rufai Hoto: @hadizel
Asali: Twitter

Babu saki ko rabuwa

Ana samun sabani a gidaje, amma a cewar Hadiza Isma El-Rufai, tun da ta auri mai gidan na ta, ba ta taba yi masa yaji, ta koma gida ba.

Wannan Baiwar Allah ta na tunkaho da cewa saki bai taba shiga tsakanin ta da mai gidanta, wanda ya zama babban ‘dan siyasa a yau ba.

Aure ya yi albarka

Kara karanta wannan

Legas: Wani Mutum Ya Mutu A Otel Bayan Sun Kwana Tare Da Budurwarsa Da Suka Hadu Ta Soshiyal Midiya

A sakamakon wannan aure ne aka haifi Yasmin El-Rufai wanda ta rasu a kasar waje a 2011.

Haka zalika matar Gwamnan ce ta haifi sauran manyan ‘ya ‘yansa irinsu Bello El-Rufai da Bashir El-Rufai wanda suka haifa masu jikoki.

Mutane a Twitter sun nuna yadda soyayyar ta burge su, irinsu Mohammed Shahi Bala da Mustapha Hodio sun bukaci uwargidar ta ba su lakanin zaman aure.

Abin ake fada a Twitter

“Alhamdulillah Mama. Allah ya kara hakuri.”

- Nafisah Sambo

Allah Ya dorar da namu auran ya fi wannan tsayi.

- @Hbbello

Sai masu cewa:

“Allah kara dankon kauna da kuma Allah kara dankon soyayya”

- Dr. Dan Hajia da Dauda Adamu Mana

Abokan zama

Legit.ng Hausa ta na da labari cewa Hadiza Isma ta na da kishiyoyi a wajen mai gidan na ta; akwai Hajiya Asiya Ahmad da kuma Aisha Ummi Garba.

Kwanakin baya aka rahoto Ummi Garba El-Rufai tace kuskuren da ake yi shi ne yi masu kallon kudi, tace sun fi shanawa kafin mijinsu ya zama Gwamna.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Peter Obi Sun Ji Zafi, Sun Kai Karar El-Rufai Wajen Kamfanin Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel