Gwamnatin Najeriya Ta Jero Jihohohin Arewa da za su yi Fama da Ambaliyar Ruwa

Gwamnatin Najeriya Ta Jero Jihohohin Arewa da za su yi Fama da Ambaliyar Ruwa

  • NiMet mai lura da yanayin gari tayi hasashe game da yadda za a karasa daminar wannan shekarar
  • Masana sun ce za ayi ruwa na marka a Kano, Jigawa, Gombe, Yobe, Bauchi da kuma Adamawa
  • Shugaban NiMet na kasa, Farfesa Mansur Matazu yace akwai yiwuwar a samu ambaliya a jihohin

Abuja - Hukumar NiMet mai lura da yanayi tayi hasashen cewa za a samu ruwan sama sosai a wasu Arewacin Najeriya, Vanguard ta kawo rahoton nan.

NiMet tace Jihohin da ruwa zai iya yin yawa a daminar bana sun hada da; Katsina, Borno, Sokoto, Kano, Jigawa, Gombe, Yobe, Bauchi sai kuma Adamawa.

Shugaban hukumar na kasa, Farfesa Mansur Matazu ya bayyana haka da ya zanta da manema labarai a ranar Talata, 16 ga watan Agusta 2022 a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Nasiru Bayero: Nasaba, Ilimi, Sana’a, Kudi da Sauran Abubuwa Game da Sarkin Bichi

A dalilin ruwan saman da za iyi karfi sosai, za a samu ambaliya a watannin Agusta, Satumba da Oktoban shekarar nan, an fara fuskantar wannan matsala.

Babu ruwan marka-marka a Kaduna dsr

Kamar yadda Darekta Janar na NiMet ya yi bayani a jiya, za a samu matsakaicin ruwan sama a Jihohi irinsu Kebbi, Zamfara, Kaduna, Nasarawa, da Taraba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wannan lokaci za a samu ruwa daidai-daidai a Legas, Ogun, Osun, Oyo da yankunan Ekiti da Edo a kudu ta yamma da tsakiyar yammacin Najeriya.

Ruwa.
Ambaliyar ruwa a Legas Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Hasashen ya nuna ruwan da za ayi a Kaduna, Adamawa, Oyo da yankunan Gombe da Ondo zai zama daidai gwargwado, ba tare da mummunar ambaliya ba.

Inda ruwan sama zai iya yin kadan

A cikin wadannan watanni uku masu zuwa, Farfesa Matazu yace a jihohin Kudu maso kudu da Kudu maso yamma, ruwan saman ba zai yi yawa sosai ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Bikin Dan Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura Da Zukekiyar Amaryarsa Yar Kasar Waje, An Sanya Masa Lalle

Wuraren da ruwa zai gaza ko kuma a samu daidai gwargwado su ne: Bayelsa, Ribas, Akwa Ibom, Kuros Riba, sai kuma Abia, Imo, Anambra, Ebonyi da Enugu.

This Day tace Mansur Matazu ya yi kira ga hukumomin da ke bada agajin gaggawa da su dage wajen daukar matakan da suka dace domin shiryawa annoba.

A jawabin da ya yi, Matazu ya bukaci a aika jami’ai zuwa wadannan yankuna domin fara fadakar da al’umma kan abin da za su yi idan ambaliya ya auka da su.

An yi shahada a Jigawa

Kun samu labari a farkon makon nan cewa ruwan sama ya yi karfi a Najeriya, har ya kashe mutum 50 a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar Jigawa.

Hukumar SEMA ta tabbatar da cewa daruruwan mutane sun rabu da gidajensu da suke nutse. A yanzu akwai magidanta da suka fake a cikin makarantu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng