Legas: Wani Mutum Ya Mutu A Otel Bayan Sun Kwana Tare Da Budurwarsa Da Suka Hadu Ta Soshiyal Midiya

Legas: Wani Mutum Ya Mutu A Otel Bayan Sun Kwana Tare Da Budurwarsa Da Suka Hadu Ta Soshiyal Midiya

  • Abdulwaheed Lamidi, wani mutum dan shekara 55 ya rasu a dakin otel bayan ya kwana da budurwarsa da suka hadu a soshiyal midiya a Legas
  • Rahotanni sun bayyana cewa budurwar mai shekara 32 ta taho daga wani gari ne bayan ya gayyace ta ya mata alkawarin zai aure ta amma da ta zo sai suka tafi otel ba gidansa ba
  • Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Legas ta bakin kakakinta SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce matar tana hannunsu ana bincike

Jihar Legas - Wani mutum mai shekara 55, Abdulawaheed Lamidi, ya rasa ransa yayin da ya kama daki a otel da budurwarsa a City International Motel, Council Bus-Stop, a Ikotun, jihar Legas.

Punch Metro ta tattaro cewa Lamidi da budurwarsa mai shekara 32 sun hadu ne a intanet bayan musayar sakonni, kuma suka amince su fara soyayya.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An yi wani mummunan hadari, ya hallaka mutane, wasu sun jikkata

Legas
Legas: Wani Mutum Ya Mutu A Otel Bayan Sun Kwana Tare Da Budurwarsa Da Suka Hadu Ta Intanet. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

An rahoto cewa soyayyar ta yi karfi har masoyan suka yanke shawarar su hadu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar The Punch ta gano cewa matar, a ranar Asabar, ta taso daga jihar da ta ke ta samu Lamidi a otel.

Masoyan sun kwana a daki guda a otel din amma da safiyar ranar Lahadi sai matsalar ta auku.

Wata majiya ta ce masoyan suna cikin dakinsu kawai sai budurwar ta fito cikin gaggawa tana neman dauki.

Ya kara da cewa da ma'aikatan otel din suka isa dakin, sun tarar da Lamidi a kwance baya motsi.

"Yarinyar ta ce mutumin na son ya shiga bandaki ne sai ya fadi a kasa. Likita da ke aiki a wani asibiti kusa da otel din da aka kira ya tabbatar mutumin ya mutu.
"Yarinyar ta zo Legas ne domin shi mutumin ya mata alkawarin zai aure ta; ta taho da kayanta kuma tana shirin zuwa gidansa ta tare. A maimakon zuwa gidansa sun fara zuwa otel kuma suna dakin ne sai ta fito tana neman dauki.

Kara karanta wannan

Matashi Dan Shekaru 27 Zai Yi Wuff Da Budurwarsa Mai Shekaru 74 Wacce Ke Tuna Masa Da Kakarsa

"Da mutane suka shiga dakin, sun same shi a kwance baya motsi. Lamarin ya faru misalin karfe 8.40 na safiyar ranar Lahadi amma yarinyar daga wata jiha ta zo. Sun hadu ta yanar gizo suka fara soyayya," majiyar ta kara.

An kai gawarsa asibiti don ajiye wa a dakin ajitar gawa yayin da yan sanda suka kama matar domin tambayoyi.

Martanin yan sanda

Kakakin yan sandan Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce wacce ake zargin ta ki yarda a tuntubi iyayenta a binciken.

Ya ce:

"Mun tuntubi iyayen marigayin kuma sun zo. Sun ce kawai a basu gawarsa. Sun ce ba za su shigar da kara ba amma rundunar yan sanda na duba bukatarsu ta sashin shari'a.
"Ba a yanke hukunci ba yanzu, amma gawar na asibiti wurin ajiya. Matar tana hannun mu amma ba ta bamu adireshin yan uwanta ba domin bata son su san abin da ya faru."

Kara karanta wannan

Budurwa ta Kaiwa Saurayi Ziyara, ya Fadi ya Mutu a Bandakin Otal, SP Benjamin Hundeyin

Wani mutum mai shekaru 42 ya mutu suna tsakar 'gwangwajewa' da budurwarsa a ɗakin otel

A wani rahoton, yan sanda a birnin Nairobi na bincike kan wani lamari da ya faru a kasar inda wani mutum mai shekaru 42 ya yanke jiki ya fadi yayin lalata da budurwarsa, LIB ta ruwaito.

An rahoto cewa Erastus Madzomba ya rasu ne a daren ranar Laraba 29 ga watan Disamba, yayin da ya ke gwangwajewa da budurwarsa mai suna Elgar Namusia a otel din Broadway Lodgings a Kawangware.

Asali: Legit.ng

Online view pixel