Fitacciyar 'yar fim: Bana zuwa coci, ni musulma ce kuma mai kishin addini na

Fitacciyar 'yar fim: Bana zuwa coci, ni musulma ce kuma mai kishin addini na

  • Shahararriyar jarumar fim, Kemi Afolabi ta jaddada cewa har gobe ita cikakkiyar Musulma ce kuma mai kishin addininta
  • Jarumar wacce ta karyata batun zuwa coci don neman warakar cutar da ke damunta ta ce akwai kusanci tsakaninta da Allah ta yadda bata bukatar wani ya gabatar da ita a gare Shi
  • A watan Maris ne dai jarumar ta ce likitanta ya sanar da ita cewa saura mata shekaru biyar a duniya

Fitacciyar jarumar fim din kudancin Najeriya wato Nollywood, Kemi Afolabi, ta karyata rade-radin cewa ta je wani sanannen coci don samun waraka daga wata cuta da ke barazana ga rayuwarta.

A watan Maris ne jarumar ta jefa dumbin masoyanta da abokan sana’arta cikin dimuwa da damuwa bayan ta ce likitanta ya fada mata a 2021 cewa saura mata shekaru biyar a duniya.

Kara karanta wannan

Ekweremadu: Takardar haihuwar matashin da zai bayar da koda ya nuna shekarunsa 21 ba 15 ba – Hukumar NIS

Wannan furuci na Afolabi ya sanya ta samun tarin sakonnin karfafawa daga shahararru, masoya da makusantanta, The Cable ta ruwaito.

'Yar Fim ta bayyana irin yadda take kaunar addinin silama
Fitacciyar 'yar fim: Bana zuwa coci, ni musulma ce kuma mai kishin addini na | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Sai dai kuma, jita-jita ya fara yawo cewa ta je wani babban coci don neman taimako. An kuma wallafa hoton wata mata wacce ta yi kama da jarumar a shafin soshiyal midiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da take martani a shafinta na Instagram a ranar Lahadi, jarumar fim din ta ce tana sane da jita-jitan kuma ta yi watsi da labarin karyar.

Ta kara da cewar ita cikakkiyar Musulma ce mai kishin addini wacce ke da alakanta musamman da Allah kuma “bana bukatar taimakon kowa don isa gare Shi."

A cewarta:

“Tunda labarin rashin lafiyata ya fito fili, Ina ta samun rahotanni marasa kan gado da na karya iri-iri.
“Na yi watsi da shi domin hankalina ya fi karkata ga samun lafiyata. Ni Musulma ce mai kishin addini wacce ta yarda da nema a wajen Allah da neman taimakonsa a lokacin bukata, wannan shine abun da nake yawan yi kuma akwai tabbacin samun farin ciki a karshe.

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyon Kyakyawar Budurwa da Tace Zata Baiwa Ɗiyar Ekweremadu Kyautar Ƙoda

“Kwanaki, akwai wani hoto da ya dunga yawo a yanar gizo ana hasashen cewa na ziyarci cocin Christ Embassy don samun waraka.
“Ban mayar da hankali kan hakan ba saboda bana kallon ziyartan coci ko samun addu’a daga fasto a matsayin aibu. Baya ga haka ddukkanmu Allah daya muke bautawa, na yarda da haka.”
Da take wallafa hoton hirarsu, ya ci gaba da cewa:
“A takaita zancen zuwa ranar Juma’a, na wallafa wani bidiyona ina addu’o’ina na Musulunci, sai ya yi wani martani mai cike da damuwa a yau yana tambayana ko yanzu na tuna cewa ni Musulma ce ko kuma ina addinin Musulunci lokacin da nake neman mafita daga cocin.
“Na cika da mamakin rashin tunani irin na mutane a kan addini wanda za a iya kallonsa a matsayin sabo.
“Ina fatan amfani da wannan kafar domin yin watsi da bayanin karyar. Ban taba halartan coci a wani lokaci don neman waraka ba. Bidiyon da ke yawo a yanar gizo ba ni bace kuma dan Allah Ina son kowa ya yi watsi da shi.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojojin Najeriya sun damke kasurgumin mai sayar wa Boko Haram kayan aiki

“Ina da alaka ta musamman da Allah, bana bukatar wani ya isar da ni zuwa gare shi.

Bidiyon tsofaffin jaruman kanywood a wajen shagalin sunan tsohuwar jaruma Fati Ladan

A wani labarin, tsohuwar jarumar masa’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Fati Ladan, ta samu karuwar diya mace a gidan aurenta.

Tuni dai aka yi shagalin suna na gani na fada, taron da ya samu halartan manyan tsoffin jaruman masana’antar da suka yi mata kara.

A cikin wani bidiyo da shafin mufeeda_rasheed1 ta wallafa a Instagram an gano tsoffin jarumar kamar su Sadiya Gyale, Fauziyya Mai kyau, Fati KK, Wasila da sauransu suna taya mai jego rawa tare da yi mata likin kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel