Babbar magana: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken gargajiya a wata jiha

Babbar magana: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken gargajiya a wata jiha

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an sace wani babban basaraken gargajiya a wani yankin jihar Ebonyi
  • Jarida ta ruwaito cewa, an sace basaraken ne a gidansa a daren Laraba, wanda har yanzu ana nemansa
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce ana ci gaba da bincike don ceto shi

Ebonyi - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken al’ummar Isuokoma mai cin gashin kansa a karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi, Eze Ambrose Ogbu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wasu da har yanzu ba a tantance ko su waye ba sun yi awon gaba da sarkin ne a daren ranar Laraba a fadarsa da ke Isu a yankin karamar hukumar.

An sace basarake a Ebonyi
Babbar magana: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken gargajiya a jihar Ebonyi | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar a Abakaliki a ranar Alhamis.

A cewar majiyar, wadanda suka yi garkuwa da sarkin ba su tuntubi danginsa ba har zuwa lokacin hada wanna rahoton, ranar Alhamis da yamma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar majiyar

“An yi garkuwa da shi a daren jiya a fadarsa. Amma masu garkuwa da mutanen ba su yi wata tattaunawa da dangi ko kuma jama’a ba. Mun kasance muna jira; amma har yanzu ba a tuntube su ba.”

Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, a ranar Alhamis ta tabbatar da faruwar lamarin, Premium Times ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Aliyu Garba, a wata tattaunawa da ya yi da wakilin Punch, a Abakaliki, ya ce ‘yan bindigar sun yi wa gidan mahaifinsa kwanton bauna ne a daren Laraba, inda suka yi awon gaba da shi.

Yayin da yake tabbatar da cewa wadanda suka yi garkuwa da sarkin ba su tuntubi iyalansa da hukumomi ba, shugaban ‘yan sandan ya ce jami’an rundunar sun gaggauta daukar matakin ganin basaraken ya sake ganawa da iyalansa.

Daya daga cikin 'yan matan Chibok: Na san marigayi Shekau, sauran mata 20 a hannun BH

A wani labarin, shekaru takwas bayan da mayakan Boko Haram suka sace ‘yan mata 276 a makarantar Sakandaren Chibok a Borno, rundunar sojin Operation Hadin Kai ta ceto wasu karin ‘yan matan Chibok biyu a dajin Sambisa.

An ce rundunar ta ceto su ne a yankin Gazuwa da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno a kwanan baya. Wadanda aka kubutar din su ne Mariam Dauda da Hauwa Joseph ne tare da jariransu, Daily Trust ta ruwaito.

Bayan ceto su sun ba da labarin wahalar da suka sha na tsawon shekaru takwas a cikin dajin a wani taron manema labarai da aka gudanar a babban dakin taro na Command-and-Control Center da ke Maimalari a Maiduguri ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel