Tsohon Sarki Sanusi II ya tanka masu rade-radin cewa yana goyon bayan Peter Obi

Tsohon Sarki Sanusi II ya tanka masu rade-radin cewa yana goyon bayan Peter Obi

  • Malam Muhammadu Sanusi II ya fito ya nesanta kansa da wani rubutu da ake yadawa da sunansa
  • Munir Sunusi Bayero ya fitar da jawabi yana cewa Mai martaba bai yi magana a kan masu takara ba
  • Hadimin tsohon Sarkin ya ce yanzu Mai martaba ya daina amfani da sunan Sanusi Lamido Sanusi

Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya ce sam bai da hannu a wani rubutu game da ‘yan takaran 2023 da mutane suke yadawa da sunansa.

Daily Trust ta ce Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya musanya wannan ne a wani jawabi da ya fitar ta hannun hadiminsa, Malam Munir Sunusi Bayero.

Munir Sunusi Bayero wanda shi ne shugaban ma’aikatan fadar Sanusi II, ya yi watsi da rubutun da ake cewa ya nuna goyon bayansa ga Peter Obi a 2023.

Sunusi Bayero yake cewa tsohon gwamnan na babban bankin kasa watau CBN bai da alaka ko ta kusa, ko ta nesa da wannan rubutu da yake yawo a shafuka.

Jawabin Munir Sunusi Bayero

“Hankalinmu ya je ga wani rubutu da yake yawo a kafofin yanar gizo, ana fashin baki kan ‘yan takara uku da suke neman shugaban kasa a zaben 2023.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Mu na so mu fada da babbar murya cewa ba Mai martaba, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya yi wannan rubutun kamar yadda ake ta faman yadawa ba.”
Mai martaba
Tsohon Sarkin Kano Sanusi II Hoto: Instagram
Asali: Instagram

“Bayan haka, mu na so mu ankarar da wadanda ba su sani ba, Khalifa yana amfani da sunan HH Muhammad Sanusi II ba kuma Sanusi Lamido Sanusi ba.”

- Munir Sunusi Bayero

Sahelian Times ta rahoto Munir Sunusi Bayero yana cewa akwai bukatar masu karatu su rika bincike, saboda gudun labaran karya da za su iya karkatarwa.

Jawabin ya kara da yin addu’a ga Allah (Subhaanahu wa Ta’aala) da ya cigaba da jagorantar lamarin Muhammadu Sanusi II domin ya taimakawa al’umma.

Legit.ng Hausa ta fahimci a wannan rubutu, an soki wasu manyan ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023, aka kuma yabi ‘dan takaran jam'iyyar LP, Peter Obi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa watau Atiku Abubakar da Asiwaju Bola Tinubu ne za su fafata a jam’iyyun PDP da APC wajen karbar mulkin Najeriya a 2023.

Tuni dai jaridar The Cable ta fitar da rahoto, ta na zargin karya aka yi wa Sanusi II a rubutun.

A tanadi katin zabe

Shehin malami, Farfesa Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya yi kira da babbar murya a kan mallakar katin zabe na PVC domin mutane su iya kada kuri'arsu.

Kamar yadda rahoto ya bayyana a farkon makon nan, Farfesan na jami’ar UDUS, Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya ce babu wani uzurin kin yin zabe a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel