Saboda tsabar kaunar Muhammadu Buhari, ya yi wa Shugaban Najeriya takwara da jaririnsa

Saboda tsabar kaunar Muhammadu Buhari, ya yi wa Shugaban Najeriya takwara da jaririnsa

  • Wani Bawan Allah da ba a bayyana sunansa ba, ya samu karuwa inda mai dakinsa ta haifi namiji
  • A shafin Facebook, Maiwada ‘Danmallam ya ce mahaifin yaron ya sa masa suna Muhammadu Buhari
  • Wannan mutumi ya zabi wannan sunan ne saboda irin kaunar da ke tsakaninsa da shugaban kasa

Nigeria - Malam Maiwada ‘Danmallam, ya bada labarin wani mutumi da ya samu haihuwa, ya kuma yi wa shugaban Najeriya takwara da wannan jaririn.

Maiwada ‘Danmallam ya bayyana wannan ne a shafinsa na Facebook a yau, Litinin 17 ga watan Junairu, 2021, inda mutane ke ta faman yi wa jaririn addu’o'i.

Kamar yadda ya fada, Danmallam yace wani abokinsa ne ya turo masa sako cewa matarsa ta haihu a ranar Larabar da ta wuce, ya sa wa yaro suna Buhari.

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

A cewar wannan mutumi da ya samu kyakkyawan yaro, kauna da soyayyar Mai girma shugaban kasa ta sa ya zabi wannan suna watau Muhammadu Buhari.

“Ina kwana mai girma jagorana. Ubangiji ya azurta ni da iyalina da samun jariri namiji a ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2022.”
“Kuma saboda irin kaunar da nake yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, na sa wa jaririn sunansa, Muhammadu Buhari.”
“Da mahaifiyar da yaron duk su na lafiya.” – Mai jego.
Muhammadu Buhari da takwaransa
Jariri Muhammadu Buhari Hoto: @maiwada.dammallam
Asali: Facebook

Shi kuwa Danmallam wanda yana daya daga cikin masoyan shugaban kasa, ya yi barka:

“Allah Ya raya mana Muhammad Buhari, Ya sa albarka a rayuwar shi. Ina taya iyalin murna."

Me jama'a suke fada?

Mutane su na ta tofa albarkacin bakinsu a game da wannan karuwa da aka samu. Yayin da wasu suke yi wa iyalin barka, wasu kuma akasin hakan su ke yi.

Kara karanta wannan

Bayan sanar da Buhari, Gwamnan APC ya bayyana dalilin da yasa zai gogayya da Tinubu a 2023

Allah Ya raya Muhammadu Buhari, Ya albarkaci rayuwarsa – Jafar Jafar
Ina fatan ba za su canza ra’ayi, su canzawa yaron suna daga baya kamar yadda wasu suka yi ba. - Yamai Mohammed
Muhammadu babban suna... Allah Ya raya shi cikin musulunci, Yayi masa albarka. Amin – Muhammad Azare
Masha Allah – Sham Faliya Sharon
Allahumma Aameen. Wasu za su ji haushin wannan abin, babu gaira babu dalili. Sai su yi ta bakin ciki! - Yusuf Muhammad Illo
Amin – SK Usman
Alhamdu lillah Allah yasa masa albarka ya rayashi rayuwar musulunci Allah yasa ya gaji halayen mai sunan gaskiya da rik'on amana.Allah ya kareshi daga sharrin zamani da na shedan a gaida mai jego muna taya ta murna da fatan alheri – Abdulrahman Masanawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel