Yadda ‘daliban aji daya suka fito da Shugabannin kasa 2, Gwamnoni 4, da Ministoci a Neja

Yadda ‘daliban aji daya suka fito da Shugabannin kasa 2, Gwamnoni 4, da Ministoci a Neja

  • Wani aji guda mai dauke da dalibai 24, ya taba yaye shugabannin kasa biyu, gwamnoni hudu, ministoci biyu, sannan kuma da Alkalai hudu a Najeriya.
  • A wannan aji har ila yau, an samu Sarakuna hudu da Jakadu zuwa kasashen waje da sauran manyan mutane da sun taba rike mukamai masu tsoka.
  • Wannan ba kowane aji ba ne sai 'yan shekarar 1957 zuwa 1962 a makarantar sakandaren gwamnati da ke Bida, jihar Neja- cikinsu har da Janar IBB.

A wani rahoto da aka fitar a News Online, an kawo jerin sunayen daliban wannan aji wanda sai da sunayensu ya ratsa kusan kowane lungu da sako a fadin Najeriya.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Janar Abdulsalam Abubakar

Janar Mamman Vatsa

Janar Mohammed Magoro

Janar Garba Duba

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Ku jira don jin ta bakinsa a watan Janairu - Fashola game da takarar Tinubu

Janar Gado Nasko

Janar Mohammed Sani Sami

Kanal Sai Bello

Daliban aji daya
Daliban makarantar Bida Hoto: www.operanews.com
Asali: UGC

Yadda 'yan ajin suka yi fice

A cikin ‘yan wannan aji ne aka yaye Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalam Abubakar wanda duk sun rike kujerar shugaban kasa a mulkin soja.

Mamman Vatsa ya zama Ministan Abuja kamar Mohammed Magoro wanda ya yi Ministan cikin gida.

Manjo Janar Gado Nasko da Laftanan Janar Garba Duba, Birgediya Mohammed Sani Sami da Kanal Sani Bello duk sai da suka yi gwamna a wasu jihohin Arewa.

Daga baya Janar Mohammed Sani Sami ya zama Sarkin Zuru. A wannan ajin ne ake da Sarkin Suleja, Auwal Ibrahim da tsofaffin Sarakunan Kontagora da na Lapai.

A bangaren shari’a, akwai Idris Legbo Kutigi, Jibrin Ndajiwo da Alkali mai shari’a, Abdullahi Mustapha.

James Tsado Kolo, Buba Ahmed, Yunusa Paiko da Abdulraham Gara sun zama Jakadu kamar yadda Jerry Gana da Awaisu Kuta, Ibrahim Tanko suka shiga siyasa.

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Shugabannin Igbo sun gana da Buhari a fadar Villa

‘Yan bokon da aka yi su ne: Farfesa Musa Abdullahi; Mohammed Dakota; A.I Kolo da M.T. A Suleiman.

Shari'ar dukiyar Abacha

A makon da ya gabata ne Alkalin wani babban kotun tarayya ya kori karar da aka shigar a gabansa domin a sa ido a kan yadda ake kashe kudin da Abacha ya sace.

Gwamnati tace za ta kashe wadannan fam $300m da aka bankado daga kasashen ketare wajen aikin hanyar Legas zuwa Ibadan da fadada titin Abuja zuwa garin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel