Daga rigima, wata mata tayi wa Mai gidanta wanka da ruwan ‘Acid’, an sheka da shi asibiti

Daga rigima, wata mata tayi wa Mai gidanta wanka da ruwan ‘Acid’, an sheka da shi asibiti

  • An ji labarin wata mata da ta watsawa mai gidanta ruwan asid a jiki, wannan ya faru ne a Benin
  • Rahotanni sun ce jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Edo sun kama matar da tayi wannan danyen aiki
  • Ma’auratan sun yi ta samun matsaloli kafin a karshe matar tayi sanadiyyar ajalin mijin aurenta

Edo - Wata mata da aka bada sunanta a matsayin Becky ta shiga cikin matsala a sakamakon zarginta da laifin watsawa mijinta ruwan asid a jiki.

Jaridar Daily Trust tace wannan mummunan abin ya faru ne a birnin Benin, a jihar Edo.

Becky ta watsawa mai gidan na ta ruwan asid mai dafi ne a sakamakon fadan da suka yi bayan sabani ya shiga tsakaninsu a gidansu da ke jihar Edo.

Read also

Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

Rahoton yace Becky ta dade tana kuka da mijin na ta mai suna Odion, wanda har ta taba kai shi gaban ‘yan sanda domin su dauki mataki a kan shi.

Jami’an ‘yan sanda sun ba matar hakuri a wancan lokaci, ta nemi ta je ta sasanta da mijinta.

Kaddara ta riga fata

An fahimci cewa ‘yanuwan ma’auratan suna neman su yi masu sulhu ne, sai kwatsam aka ji matar ta watsawa mijinta asid a karshen makon jiya.

Ruwan ‘Acid’
Kwalbar asid a dakin bincike Hoto: www.thoughtco.com
Source: UGC

Majiyar tace da makwabta suka ji Odion yana ihu, sai suka garzayo gidansu domin kawo masa agaji, sai kurum aka same shi a kwance, yana ta birgima.

Matar da tayi wannan abin ta shiga hannun hukuma, tuni ‘yan sandan garin Benin suka cafke ta. Amma ‘yanuwan mamacin su na cewa matar ta tsere.

Read also

Amotekun ta kama mai garkuwa da mutane Labram Ibrahim yayin da yake haukan karya a Ondo

Da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba, 2021, ta bayyana cewa za ta fitar da cikakken jawabin kan abin da ya auku.

Odion ya mutu a asibiti

Wani rahoto daga Express News yace Odion ya rasu bayan ya yi fama da ‘yar jinya. Magidancin ya rasu ne a asibitin koyar da aikin likitoci na jami’ar Benin.

‘Yar uwar marigayin, Esohe Fidelis tace dama matar tace sai ta ga bayan Odion, ga shi nan tayi nasarar kashe shi, ya mutu ne sa’a 12 bayan abin da ya farun.

Binciken #LekkiGate ya fito

A makon yau aka ji kwamiti na musamman da gwamnatin jihar Legas ta ba alhakin binciken abin da ya faru a lokacin zanga-zangar #EndSARS ya gama zama.

Kwamitin binciken yace shakka babu sojoji sun yi wa jama'a kisan gilla. Bayan sojoji sun buda wuta, sun kashe mutane, boye gawawwaki, kuma sun boye harsasai.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel