EndSARS: Bayan shekara 1, bincike ya tona abin da ya faru a Lekki, an zargi Sojoji da kisan kiyashi

EndSARS: Bayan shekara 1, bincike ya tona abin da ya faru a Lekki, an zargi Sojoji da kisan kiyashi

  • Binciken EndSARS da kwamitin da Gwamnatin Legas ta kafa ya yi, ya zargi jami’an tsaro da kisan gilla
  • Rahoton kwamitin Doris Okuwobi ya tabbatar da cewa sojoji sun hallaka ‘yan zanga-zanga a kofar Lekki
  • Sojoji sun buda wuta sun kashe mutane rututu, sannan suka boye gawawwakinsu domin ayi rufa-rufa

Lagos - Kwamiti na musamman da gwamnatin jihar Legas ta ba alhakin binciken abin da ya faru a lokacin zanga-zangar #EndSARS ya kammala aikinsa.

VOA Hausa tace binciken kwamitin ya bada tabbacin cewa jami’an tsaro sun kashe wasu daga cikin wadanda suka yi zanga-zanga a kofar shiga Lekki.

Kwamitin da Alkali Doris Okuwobi ta jagoranta ya tabbatar da cewa sojoji sun buda wuta ga masu zanga-zanga a bakin kofar shiga wannan unguwa a Legas.

Hakan ya sa tsautsayi ya yi sanadiyyar mutuwar wasu da suka fito zanga-zangar lumana domin yin Allah-wadai da zaluncin jami’an ‘yan sanda a Najeriya.

Matasan sun zargi dakarun SARS da zalunci, suka ce su na tare mutanen da aka gani dauke da komfuta, ana jifarsu da zargin damfara, har a harbi wasunsu.

EndSARS
Masu zanga-zangar EndSARS Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamiti ya gabatar da dogon rahoto

Wannan rahoto mai shafuka sama da 300 da kwamitin binciken ya gabatar, ya bayyana yadda jami’an tsaro suka aukawa masu zanga-zangar ta lumuna.

Rahoton yace jami’an tsaron da ake zargi da laifi sun hada da sojojin kasa da dakarun ‘yan sanda.

Ta'adin da jami'an tsaro suka yi a Lekki

Jami’an tsaro sun harbi Bayin Allah barkatai a wajen wannan zanga-zanga, bayan haka suka dauke gawawwakin da harsasan bindiga, domin birne sawunsu.

Kwamitin yace a ranar 20 ga watan Oktoban 2021, sojoji sun buda wuta ga mutanen da ba su rike da wani makami sai tutar Najeriya, suna rera taken kasarsu.

Wannan kwamiti na musamman ya zargi jami’an tsaro da hana bada motocin asibiti, a taimakawa masu rauni, a karshe ya ba gwamnati shawarwari.

Shawarar da MURIC ta ba masu zanga-zanga

A lokacin da aka ruguza dakarun SARS saboda zargin da ake yi mata, kungiyar nan MURIC ta yi magana ta na kiran a janye zanga-zangar #EndSARS da ake yi.

MURIC mai wayar da kan jama’a kan hakkokin musulmai, ta gargadi masu wannan zanga-zanga da cewa su yi hattara da mugun nufin wasu da suka shiga rigarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel