Wani ɗan sanda ya kashe abokan aikinsa 'yan sanda 4, ya kuma yi wa wasu 3 mummunan rauni

Wani ɗan sanda ya kashe abokan aikinsa 'yan sanda 4, ya kuma yi wa wasu 3 mummunan rauni

  • Wani dan sanda mai suna Reetesh Ranjan ya bindige abokan aikinsa 4 har lahira ya kuma raunata wasu guda 3
  • Lamarin ya faru ne a sansanin yan sandan CFRF ta bataliyya ta 50 da ke kauyen Linganpalli a ranar Litinin
  • Tuni dai mahukunta sun yi nasarar kama Ranjan domin bincike amma a halin yanzu ba a san dalilin da yasa ya yi harbin ba

India - Wani jami'in dan sanda a kasar Indiya a karkashin CRPF, a ranar Litinin ya bude wa abokan aikinsa hudu wuta a tsakiyar jihar Chhattisgarh, inda ya kashe hudu ya raunata uku.

Kafafen watsa labarai na Indiya sun ruwaito cewa lamarin ya faru ne a sansanin CRPF, bataliya na 50 da ke kauyen Linganpalli a karkashin caji ofis na Maraiguda misalin karfe 3.15 na safen Litinin (21:45 agogon GMT).

Kara karanta wannan

Sabon hoton Mufti Menk sanye da babbar riga ya janyo cece-kuce

Wani dan sanda ya kashe abokan aikinsa 'yan sanda 4, ya kuma yi wa wasu 3 mummunan rauni
Wani dan sanda ya kashe abokan aikinsa 'yan sanda 4, ya kuma yi wa wasu 3 rauni. Hoto: Vanguard NGR
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa binciken farko-farko da aka fara yi, an gano cewa Constable Reetesh Ranjan, ya bude wa abokan aikinsa wuta ne da bindigar AK-47.

An garzaya da mutanen da ya harba asibiti inda a can likitoci suka tabbatar da cewa hudu daga cikinsu sun riga mu gidan gaskiya.

Sauran ukun suna can asibiti suna samun kulawar likitoci.

An kama Rajaan domin fara bincike

Daga bisani an kama shi bayan da ya yi harbin.

NDTV ta ruwaito cewa tuni an fara bincike domin gano abin da ya harzuka shi har ya yi wannan mummunan abin.

'Dan sanda ya daɓa wa abokin aikinsa wuƙa ya yi sanadin ajalinsa

A wani labari mai kama da wannan, kun ji ana zargin wani dan sanda, Sajan Akpoboloukeme da halaka abokin aikin sa, Sajan Sapele Eyerindideke wanda ya kai ga halaka shi.

Kara karanta wannan

Hoton karshe na ginin da ya rubto a Legas: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da wannan gini

Ganau sun bayyana yadda lamarin ya auku a ranar Alhamis da yamma a yankin Edepie da ke Yenagoa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Abokan aikin su sun shaida yadda wata karamar hayaniya ta shiga tsakanin su kafin lamarin ya kazanta.

An samu rahotanni akan yadda wanda ya yi kisan ya yi gaggawar rantawa a na kare bayan ya gane cewa wanda ya datsa ya mutu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel