'Dan sanda ya daɓa wa abokin aikinsa wuƙa ya yi sanadin ajalinsa

'Dan sanda ya daɓa wa abokin aikinsa wuƙa ya yi sanadin ajalinsa

  • Wani dan sanda, Sajen Akpoboloukeme ya sari abokin aikin sa, Sajen Sapele Eyerindideke, wanda hakan ya kai ga ajalin sa a Yenagoa, jihar Beyelsa
  • Kamar yadda ganau su ka tabbatar, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da yamma a yankin Edepie da ke Yenagoa bayan wata sa-in- sa ta shiga tsakanin su
  • Kamar yadda abokan ‘yan sandan su ka shaida, sun je wani biki ne a yankin Yenagoa inda mamacin ya ja wanda ya halaka shi da wasa ashe wasan be yi ma sa dadi ba

Jaihr Bayelsa - Ana zargin wani dan sanda, Sajan Akpoboloukeme da halaka abokin aikin sa, Sajan Sapele Eyerindideke wanda ya kai ga halaka shi.

Ganau sun bayyana yadda lamarin ya auku a ranar Alhamis da yamma a yankin Edepie da ke Yenagoa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da mijin da ya soka wa matarsa almakashi, ta sheka lahira

'Dan sanda ya daɓa wa abokin aikinsa wuƙa ya yi sanadin ajalinsa
'Dan sanda ya daɓa wa abokin aikinsa wuƙa ya yi sanadin mutuwarsa. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abokan aikin su sun shaida yadda wata karamar hayaniya ta shiga tsakanin su kafin lamarin ya kazanta.

An samu rahotanni akan yadda wanda ya yi kisan ya yi gaggawar rantawa a na kare bayan ya gane cewa wanda ya datsa ya mutu.

Daga baya aka kama shi a wuraren Glory Land, hanyar da mutum zai fita daga Yenagoa.

Mamacin da makashin su na da alaka ta jini

An tattaro bayani akan yadda su biyun su ke da alaka ta jini don ‘yan asalin garin Torubene ne da ke jihar Delta.

Abokan su sun bayyana yadda mamacin ya ja Akpoboloukeme da wasa yayin da su ke zaune a wani biki da su ka je wani fitaccen otal da ke kan titin INEC.

Dama an yi wa makashin shaidar ya na da zuciya, ya yi saurin hassala bayan mamacin ya ja shi da wasa, daga nan ya datse shi.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sintiri sun yi ram da mutumin da ke bayyana wa mata al'aurarsa

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce an kama makashin kuma ana ci gaba da bincike.

Ya kara da cewa:

“Wani dan sanda wanda ba ya bakin aiki sa ya datsi abokin aikin sa inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sa har lahira a Yenagoa bayan wani karamin rikici ya shiga tsakanin su.
“Lamarin ya auku ne a ranar 4 ga watan Nuwamban 2021 da misalin karfe 5 na yamma a Edepie da ke Yenagoa.
“An samu rahoto akan yadda Akpoboloukeme datsi abokin aikin na sa, Sajan Sapele Eyerindideke akan wani karamin rikici.
“Yanzu haka an mayar da gawar mamacin zuwa ma’adanar gawa don kara bincike akan lamarin.”

An zargi wanda ya yi aika-aikar da yunkurin tserewa amma an yi gaggawar damkar sa a Glory Land Gate.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bayelsa, CP Ben Okolo, ya umarci a rike makashin kuma a gudanar da bincike mai zurfi akan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel