Latest
Zaben fitar da gwani ya zo tangarda yayin da Sanatoci 3 da ‘Yan Majalisa suka sha kasa. A cikin duka Sanatocin Jigawa, babu wanda zai koma kan kujerarsa a APC.
Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi watattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da dan takarar shugabancin kasa na APC Sanata Rochas Okorocha.
Wani 'dan Najeriya mai shekaru 36 da ke zaune a Italy, Nwakanma Uche, ya kasayar da sunkin kwayar heroin guda 95, bayan jami'an NDLEA sun tistiye shi a Abuja.
Bincike da hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ke yi kan dakataccen Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris, ya kai biliyan B170.
Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya yabawa Gwamna Aminu Tambuwal, kan rawar ganin da ya taka a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar da aka yi.
Kanal Abdulaziz Musa ‘Yaradua ya samu tikitin takarar Sanata a bangaren Katsina ta tsakiya. APC ta canza wadanda za su yi mata takarar Sanata a Kudu da Arewa.
Tare da taimakon jami'an tsaro na jihar Adamawa, an gano inda 'ya'ya 8 na 'yan ta'addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Kaduna suke da taimakon Tukur Mamu.
Yayin da APC za ta gudanar da zaben ‘dan takarar shugaban kasa a makon gobe. Shugaban kasa ya nesanta kansa daga zargin kakaba Jonathan a matsayin ‘dan takara.
Rundunar 'yan sandan jihar Kogi a ranar Lahadi ta tabbatar da fashewar wani abu a wani gidan giya da ke garin Kabba da ke karamar hukumar Kabba-Bunu ta jihar.
Masu zafi
Samu kari