Latest
A wani rubutun da ya yada, Ali Nuhu ya yiwa Davido tofin Allah-tsine game da bidiyon da ya yada na yadda ake wasa da ana tika rawa a masallaci a cikin gari.
Jerin gwanon motocin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki sun makale akan hanyar Sapele bayan tafka ruwa kamar da bakin kwarya a birnin, mutane sun yi martani.
Babban malamin addinin nan kuma shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya yi wani sabon hasashe mai hadarin gaske kan ƴan kasuwar man fetur a ƙasar nan.
A yayin da ake ci gaba da koka wa kan raɗaɗin cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi, gwamnatin jihar Ebonyi ta shirya share hawayen al'ummar jihar.
Masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara sun yi barazanar auren 'yan mata hudu da ke hannunsu idan har iyayensu ba su biya kudin fansa N12m nan da mako daya ba.
'Yan sanda sun cafke dalibai su 10 da suka ci zarafin malami bayan ya hana su satar amsa a jarabawa a jihar Ogun, sun tare shi ne bayan an tashi a makaranta.
Gwamna Charles Chukwuma Soludo ya yi bayanin abin da Gwamnoni su ka tattauna a Aso Rock, ya bada misalin yadda ya rage barnar kudi da shawarar da aka kawo a NEC
Lauyan dimokradiyya ya bayyana abubuwan da aka bankado a gidan tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele. Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi dashi jiya.
Musulmai da Kiristocin jihar Borno sun gudanar da sallar rokon ruwa a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. Hakn ya biyo bayan yadda aka ga damina ta dauke.
Masu zafi
Samu kari