Dirama Yayin da Kotu Ta Hana Cafke Shugaban Ma'aikatan Gwamnan PDP Kan Abu 1 Tak

Dirama Yayin da Kotu Ta Hana Cafke Shugaban Ma'aikatan Gwamnan PDP Kan Abu 1 Tak

  • Rikicin da ya dabaibaye majalisar dokokin jihar Rivers bai zo ƙarshe ba duk da m matakin da Gwamna Fubara ya ɗauka na son kawo zaman lafiya
  • A ranar Laraba wata babbar kotu da ke birnin tarayya Abuja, ta bayar da sammacin kama shugaban ma’aikatan Fubara, Edison Ehie, kan ƙona ginin majalisar dokokin jihar
  • A wani mataki na gaggawa, babbar kotun jihar Rivers ta bayar da umarni wanda ya ƙalubalanci hukuncin da kotun ta yanke a kan Ehie

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Biyo bayan rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar Rivers, babbar kotun jihar Rivers, reshen Port Harcourt, ta bayar da umarnin hana rundunar ƴan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro cafke Edison Ehie.

Kara karanta wannan

Duk da suka daga 'yan Arewa ministan Tinubu ya dage kan mayar da FAAN zuwa Legas, ya fadi dalili

Jaridar The Punch ta ce umurnin ya biyo bayan ƙorafin da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Rivers, ya shigar a gabanta.

Kotu ta hana cafke Ehie
Kotu ta hana ƴan sanda cafke Edison Ehie Hoto: Edison Ehie, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Edison Ehie ya nemi a hana ƴan sanda kama shi bisa zarginsa da hannu wajen ƙona zauren majalisar dokokin jihar Rivers a shekarar 2023, cewar rahoton Channels Tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hana cafke Ehie dai na zuwa ne bayan wata babbar kotu tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin a cafke shi.

Yadda wani abu ya fashe a majalisar dokokin jihar Rivers

Ku tuna cewa a daren Lahadi, 29 ga Oktoba, 2023, an samu fashewar wani abu a harabar majalisar dokokin jihar Rivers.

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake zargin wasu ƴan majalisar dokokin jihar na yunƙurin tsige Gwamna Sim Fubara.

Fashewar ta tilastawa gwamnatin Rivers rusa majalisar dokokin jihar.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta bada umarnin kama shugaban ma'aikatan gwamnan PDP da wasu mutum 5 kan abu 1 tak

Kotu ta hana a cafke Edison Ehie

Sai dai a ranar Laraba, 31 ga watan Janairu, 2024, alƙalin kotun, Sika Aprioku, ya bayar da umarnin hana cafke Edie, kafin ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Fabrairun 2024.

Tawagar da Martin Amaewhule ke jagoranta ta kai ƙara inda ta buƙaci a kama Ehie, a gudanar da bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da hannu wajen ƙone-ƙonen da aka yi a harabar majalisar.

Majalisa Ta Juya Wa Fubara Baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Rivers ta zartar da wasu ƙudurori sun zama doka ba tare da amincewar Gwamna Siminalayi Fubara ba.

Majalisar ta cimma hakan ne bayan ƴan majalisar sun yanke shawarar kaɗa ƙuri'ar yin watsi da gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel