Latest
Sodiq Adebisi, wani dan wasan tamaula a jihar Ogun ya riga mu gidan gaskiya jim kaɗan bayan ya yanku jiki ya faɗi ana tsaka da ɗaukar horo a filin wasa.
Hafsan sojin Najeriya, Manjo-Janar Taoreed Lagbaja ya karrama dakaru 86 saboda kwarewar aiki da kuma nuna bajinta a jarabawar karin girma da aka yi musu.
Kungiyar nan mai fafutukar kare hakkin Musulmai MURIC ta buƙaci Gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike mai tsafka kan abin da ya jawo kisan masu maulidi a Kaduna.
Wani dan Najeriya ya shiga hannun yan sanda a kasar Burtaniya bayan ya salwantar da ran matarsa wacce suka kwashe shekara 17 suna rayuwar aure tare.
Jam'iyyar PDP ta fara farfaɗowa da nufin warware dukkan rigingimun cikin gida, ta umarci mambobinta su garzaya su janye kararrakin da suka shigar gaban kotu.
Rundunar 'yan sanda ta sanar da nasarar da dakarunta suka samu na afke masu laifi 130 a jihar Katsina a cikin watan Nuwamba. Tuni ta gurfanar da mutum 61.
Sanatan Kaduna ta kudu, Sunday Marshall Katung, ya ce zai haɗa kai da sauran yan majalisar tarayya na jihar domin kwato hakkin mutanen da aka kashe a Tudun Biri.
Miyagun ƴan bindiga sun salwantar da rayukan mutum 33 a wani sabon hari da suka kai a ƙaramar hukumar Bali ta jihar Nasarawa. Sun kuma sace dabbobi.
Wata baturiya mai shekaru sittin da biyu ta samu nasarar yin saukar Al-Kur'ani a wata makarantar islamiyya a Kano. Shekarunta talatin kenan a jihar Kano.
Masu zafi
Samu kari