Latest
'Yan bindigar da suka yi awon gaba da daliban makaranta a jihar Ekiti sun rage kudin fansarsu zuwa naira miliyan 15.Sun yi barazanar kashe su idan ba a biya ba.
Mazauna wasu garuruwan da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna sun tsere daga gidajensu saboda fargabar harin miyagun ‘yan bindiga da suka shigo yankin.
Ministan yada labarai Najeriya, Mohammed Idris ya kare matakin cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Mayun shekarar 2023 a Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa zanga-zanga ta ɓarke a jihar Katsina bayan wani mutumi, Mani Habu ya yi kalaman ɓatanci ga addinin Musulunci a jihar Katsina.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya roƙi al'ummar mazaɓun da za a yi zaben cike gurbi su nuan wa APC cewa sun gaji da ita a jihohi 9.m~
Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed Kauran Bauchi ta musanta taimakawa wajen kama Sheikh Abdul'aziz Idris Dutsen Tanshi.
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun damƙe mutane 13 da ake zargi suna da hannu a kisan da aka yi wa sarakuna 2 ranar Litinin a jihar Ekiti.
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta hana dan takarar sanatan PDP tsayawaa zaben cike gurbi da za a yi a ranar Asabar 3 ga watan Faburairu a fadin kasar.
Yunkurin kawo karshen ta'addanci da tsagerancin 'yan bindiga ya yi nisa. Gwamnatin Najeriya ta saye jiragen AH-1Z da kayan yaki daga hannun Amurka.
Masu zafi
Samu kari