Latest
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta yi kuskuren cire sunan PDP a jerin jam'iyyu yayin da ake rarraba kayan zaben cike gurbi da ake shirin yi a ranar Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa an tsinto gawarwakin mutane 15 yanzu haka bayan wani hari da aka kai mai muni kan jama'a a yankin karamar hukumar Agatu, jihar Benue.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shaida cewa an hana su mu’amala da kudinsu da ke banki. Dabarar shi ne za a janye kudi a duk lokacin da suka shigo.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Fayode Adegoke, ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane domin yin hakan kuskure ne.
Miyagun 'yan bindigan da suka sace wasu mutum bakwai a babban birnin tarayya Abuja, sun fadi makudan kudaden fansan da za a ba su kafin su sako mutanen.
Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta nada Hon. Amina Arong Divine a matsayin shugabar matan jam'iyyar bayan mutuwar tsohuwar shugabar matan, Farfesa Stella.
'Yan kasuwar canji (BDC) sun sanar da dakatar da aiki a Abuja sakamakon rashin samun wadatattun takardun dalar Amurka daga ranar 1 ga watan Fabreru.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun sake kai harin ta'addanci a birnin tarayya Abuja, 'yan bindigan a yayin harin sun yi awon gaba wani babban darakta.
Ministan wutar lantarki a Najeriya, Adebayo Adelabu ya bukaci cire tallafin wutar kantarki don samar da ita yadda ya kamata ganin yadda basuka suka yi yawa.
Masu zafi
Samu kari