An Bai Wa Ministan Tinubu Sarautar 'Sarkin Yaƙi' Yayin da Ake Fama da Matsalar Ƴan Bindiga

An Bai Wa Ministan Tinubu Sarautar 'Sarkin Yaƙi' Yayin da Ake Fama da Matsalar Ƴan Bindiga

  • An bai wa ministan Abuja, Nyesom Wike rawanin sarauta 'Sarkin Yaƙi' a wani yankin ƙaramar hukumar Gwagwalada da ke birnin tarayya
  • Aguma na Gwagwalada, Cif Mohammed Magaji ne ya sanar da haka ranar 1 ga watan Janairu lokacin da Wike ya je kaddamar da aikin titi
  • Basaraken ya yabawa Wike bisa dumbin ayyukan da ya zuba wa yankunan karkara a dan kankanin lokaci da hawansa kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wani yanki a ƙaramar hukumar Gwagwalada da ke Abuja ya naɗawa Nyesom Wike, ministan Abuja rawanin sarauta na, 'Sarkin Yaƙi'.

Aguma na Gwagwalada, Cif Mohammed Magaji ne ya bayyana haka ranar Alhamis, 1 ga watan Janairu, 2024, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dirama yayin da kotu ta hana cafke shugaban ma'aikatan gwamnan PDP kan abu 1 tak

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Ana Tsaka da Fama da Yan Bindiga, Wike Ya Samu Mukamin Sarauta a Abuja Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Basaraken ya sanar da bai wa Wike wannan sarauta ta Sarkin Yaƙi ne yayin da ministan ya ziyarci yankin domin kaddamar da ginawa da gyara titin Paikon Kore-Ibwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basaraken Abuja ya yabawa Wike

Magaji ya yabawa Mista Wike bisa ayyukan raya ƙasa da ya fara zubawa a yankunan karkara cikin kanƙanin lokacin bayan ya shiga Ofis.

Ya kuma faɗa wa ministan cewa suna tsammanin zai amince da wannan sarauta da aka ba shi domin fara shirye-shiryen bikin naɗa rawani.

Da yake miƙa godiya ga ministan bisa daukar kwararan matakan bunkasa karkara a FCT, Magaji ya yi fatan cewa aikin zai saukaka rayuwa da kawo ci gaban yankin.

Wike ya jaddada ajendar Tinubu

Da yake kaddamar da aikin, Wike ya ce wannan aikin wani bangare ne na tituna masu tsawon kilomita 30 da za a gina a fadin kananan hukumomi shida na Abuja.

Kara karanta wannan

Duk da suka daga 'yan Arewa ministan Tinubu ya dage kan mayar da FAAN zuwa Legas, ya fadi dalili

Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa ajandar da Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya zo da ita 'Renewed Hope" ba iya magana kaɗai bace sai dai a ga a aiki a ƙasa.

A cewarsa, za a yi wannan aikin titin ne domin mazauna yankunan su rayu cikin jin daɗi da kuma buɗe musu ƙofofin samun ci gaba.

Sarautar da aka ba Wike na zuwa ne a lokacin da matsalar tsaro ta dabaibaye Abuja, inda a ƴan kwanakin nan masu garkuwa ke cin karensu babu babbaka.

Najeriya Ta Sayo Jiragen $1bn Daga Kasar Amurka

A wani rahoton na daban kun ji cewa Sojojin Najeriya za su samu jiragen AH-1Z masu saukar ungulu wadanda suka yi fice a barin wuta.

Ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta tabbatar da ciniki tsakaninta da Najeriya domin magance matsalar ta’addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel