Latest
Wasu mata da ke yin gurasa a Kano, sun yi zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu kan karin kudin fulawa, sun ce karin kudin ya jefa sana'arsu cikin wani hali.
Shugaba Tinubu ya karfafi guiwar Super Eagles a yayin da take shirin buga wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) da Angola.
Ahmed Musa ya na cikin kwararrun ‘yan wasan Super Eagles wadanda aka dade ana yi da su. Musa ya fadawa 'yan kwallon Najeriya yadda za ayi nasara a kan Angola.
Gwamnonin jam'iyyar PDP sun ziyarci al'ummar jihar Filato da hare-haren 'yan bindiga ya ritsa domin jajanta masu. Sun bayar da gudunmawar naira miliyan 100.
Majalisar jihar Oyo ta bukaci cafke shugaban Fulani, Seriki Chumo kan zargin kisan manomi da jami'in tsaron Amotekun a yankin Iwajowa da ke jihar.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi ta'aziyyar rasuwar Haja Hauwa, matar mahaifin mataimakin shugaban ƙasa wanda ta rasu ranar Alhamis a Maiduguri.
Wani dan sanda ya gamu da ajalinsa a ranar Alhamis a jihar Ebonyi lokacin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta kan tawagar ‘yan sanda da ke sintiri.
Ma'aikatan tarayya sun fara 'yan guna-guni yayin da gwamnati ta gaza cika alkawarin da ta dauka na yin albashi a ranar Alhamis, kuma ba a biya su naira dubu 35 ba.
Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya tsere daga Bauchi ya bar jami’an tsaro 250 suna neman shi. Lauyan Dutsen Tanshi ya fadi abin da yake faruwa da malamin.
Masu zafi
Samu kari