Gwamnonin PDP Sun Ba Mutanen da Hare-Haren Filato Ya Ritsa da Su Gudunmawar Miliyan 100

Gwamnonin PDP Sun Ba Mutanen da Hare-Haren Filato Ya Ritsa da Su Gudunmawar Miliyan 100

  • Kungiyar gwamnonin PDP sun ba wadanda hare-haren 'yan bindiga ya ritsa da su a jihar Filato gudunmawar naira miliyan 100
  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya jagoranci takwarorinsa na PDP zuwa gidan gwamnatin Filato domin yi wa Gwamna Caleb Mutfwang da mutanen Filato jaje
  • Gwamnan Bauchin ya yi kira ga kafa 'yan sandan jiha, tare da nuni ga muhimmancin hadin kai a tsakanin al'umma don samun zaman lafiya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kungiyar gwamnonin PDP ta bayar da gudunmawar naira miliyan 100 don tallafawa wadanda hare-haren 'yan bindiga ya ritsa da su a jihar Filato.

Miyagun 'yan bindiga sun kai hare-hare jihar wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka masu yawan gaske da miliyoyin naira.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Gwamnan Arewa ya sanar da wani muhimmin aiki da zai yi nan da 2027

Gwamnonin PDP sun ba wadanda harin Filato ya ritsa da su miliyan 100
Gwamnonin PDP Sun Ba Mutanen da Hare-Haren Filato Ya Ritsa da Su Gudunmawar Miliyan 100 Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Gwamnonin sun bayar da gudunmawar kudin ne a lokacin da suka kai ziyarar nuna goyon baya ga Gwamna Caleb Mutfwang a gidan gwamnati da ke Rayfield, Jos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun kuma yi nuni da cewa hakan zai taimaka wajen farfado da yankunan da abin ya shafa.

Ya kamata a kafa 'yan sandan jiha, Bala Mohammed

Gwamnonin sun samu goyon bayan shugaban kungiyar, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.

Da yake jawabi, Mohammed ya jajantawa Gwamna Mutfwang da mutanen jihar Filato.

Ya yi kira da a mayar da hankali wajen samar da tsaro tare da kafa ‘yan sandan jiha, yana mai nuni da cewa akwai bukatar samun hadin kai.

Mutfwang ya nuna jin dadinsa ga takwarorinsa kan wannan ziyara da suka kai masa, cewa muhimmancin ziyarar a lokacin da jihar ke fuskantar kalubale akwai sanyaya zuciya.

Kara karanta wannan

Musulmai sun cire tsoro, sun bayyanawa gwamnan APC ido da ido bukatarsu kan nade-naden gwamnati

An kashe mutum 91 a Filato

A wani labarin, mun ji cewa shugaban kungiyar matasan Mwaghavul na kasa, Kwamared Sunday Dankaka, ya ce mutane 91 ne suka mutu a rikicin da ya barke a karamar hukumar Mangu a makon jiya.

Kwamared Ɗankaka ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Jos, babban birnin jihar Filato, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce waɗanda rikicin Mangu ya yi sanadin mutuwarsu a makon jiya sun kunshi mata 42, ƙananan yara 37, da magidanta maza 12.

Asali: Legit.ng

Online view pixel