Sufetan Ƴan Sanda Ya Bada Umarnin Takaita Zirga-Zirga a Legas, Kano da Wasu Jihohi 24 Kan Abu 1

Sufetan Ƴan Sanda Ya Bada Umarnin Takaita Zirga-Zirga a Legas, Kano da Wasu Jihohi 24 Kan Abu 1

  • IGP Kayode ya bada umarnin taƙaita zirga-zirgan ababen hawa a jihohi 26 da za a yi zaben cike gurbi ranar Asabar
  • Shugaban rundunar ƴan sandan ya hana zirga-zirga daga ƙarfe 12:00 na dare zuwa 6:00 na safe a waɗannan jihohi da suka kunshi Legas da Kano
  • Ya kuma haramtawa dogaran manyan mutane raka iyayen gidansu zuwa rumfunan zaɓe ko wurin harhaɗa sakamako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin taƙaita duk wani nau’in zirga-zirgar ababen hawa a kan tituna, hanyoyin ruwa da sauran hanyoyin sufuri a jihohi 26.

Sufetan ƴan sandan ya bada umarnin hana zirga-zirgan dukkan nau'in sufuri daga ƙarfe 12:00 na dare zuwa 6:00 na safiya jihohi 26 da za a gudanar da ƙarishen zaɓe ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana ƴan takarar da yake goyon baya a zaben da za a yi ranar Asabar a jihohi 9

Sufetan ƴan sanda na ƙasa.
IGP Ya Bada Umarnin Taƙaita Zirga-Zirga a Jihohin Legas, Kano da Wasu 24 Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Sai dai umarnin ya ware wasu waɗanda hanin bai hau kansu ba kamar jami'an hukumar zaɓe INEC, masu sa ido na gida da na waje, ƴan jarida, motocin ujila, ƴan kwana-kwana da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin IGP bai shafi waɗannan rukunin mutanen bane saboda kai agajin gaggawa a lokacin da aka buƙata yayin zaɓen.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da rundunar ta wallafa a manhajar X ranar Alhamis.

Jihohin da IGP ya taƙaita zirga-zirga

Jihohin da wannan mataki na taƙaita zirga-zirga ya shafa sun haɗa da Ebonyi, Yobe, Kebbi, Laegas, Ondo, Taraba, Benuwe, Borno, Kaduna, Filato da kuma Akwa Ibom.

Sauran sune, Anambra, Kuros Riba, Delta, Enugu, Jigawa, Katsina, Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Kano, Nasarawa, Neja, Oyo, Sakkwato, da Zamfara.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke kasurgumin shugaban ƴan bindiga a Arewa, sun ceto mutum 20 da aka sace

Bugu da ƙari, IGP ya hana duk wasu jami'an tsaron da ke tare da manyan mutane da kar su kuskura su raka iyayen gidansu zuwa rumfunan zaɓe ko wurin tattara sakamako.

Sanarwan ta ce:

"IG ya roƙi jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da magoya bayansu su yi taka tsantsan da kiyaye duk abinda za su aikata kuma su tabbata suna bin dokokin zabe.
"Duk wani yunƙuri na kawo cikas ga tsarin gudanar zaɓe ko karya ƙa'idojin da aka gindaya, zai fuskanci cikakken ƙarfin doka."

An yi wa ministan Abuja sarautar Sarkin Yaƙi

A wani rahoton kuma An bai wa ministan Abuja, Nyesom Wike rawanin sarauta 'Sarkin Yaƙi' a wani yankin ƙaramar hukumar Gwagwalada da ke birnin tarayya.

Aguma na Gwagwalada, Cif Mohammed Magaji ne ya sanar da haka ranar 1 ga watan Janairu lokacin da Wike ya je kaddamar da aikin titi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel