Lauya Ya Fadi Inda Sheikh Abdulaziz Dutsen Tanshi Ya Boye da Ake Neman Shi Ido Rufe

Lauya Ya Fadi Inda Sheikh Abdulaziz Dutsen Tanshi Ya Boye da Ake Neman Shi Ido Rufe

  • Zuwa yanzu an rasa ina Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya shiga bayan an bada izinin a cafke shi
  • Lauyan malamin ya zargi hukuma da taso shi a gaba, ikirarin da gwamnatin Bauchi ta karyata
  • Ahmad Musa ya ce malamin ya samu wani amintaccen wuri ya boye domin ya gujewa daure shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Bauchi - Fitaccen malamin musuluncin nan, Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya boye yayin da kotu ta bada umarnin a cafke shi.

Wani rahoton Premium Times ya tabbatar da cewa Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi yana wasan buya da hukumar a garin Bauchi.

Jami'an tsaro - Dutsen Tanshi
Ana neman Sheikh Abdulaziz Dutsen Tanshi (Hoton bai da alaka da labarin) Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tun a ranar 24 ga watan Junairu, jami’an tsaro suka shiga gidan babban malamin da nufin cafke shi, har yanzu ba su yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Rikita-rikita yayin da tsohon Akanta-janar ya tona asirin EFCC kan yarjejeniyarsu, ya fadi dalilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan da yake kare malamin a kotu, Ahmad Musa ya shaidawa jaridar cewa ya boye ne ganin yadda gwamnatin Bauchi ta taso shi.

A cewar Musa, da gan-gan ake ba su tsauraran sharudan beli saboda a rufe malamin.

Ina Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi?

"Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi ya bar Bauchi ya tsere domin gudun a zalunce shi kuma a cafke shi haka kurum.
"Gwamnatin Bauchi na neman rufe shi a kan zargin yin batanci ga addinin musulunci.
"(Dutsen Tanshi) ya yi nasarar barin Bauchi zuwa inda ya samu kubuta."

- Ahmed Musa

Lauyan yake cewa duk da shari’ar da ke kotun daukaka kara, alkalin babban kotun shari’a, Hussaini Turaki ya bada damar cafke shehin.

Saboda wannan dama ne aka zo da jami’an ‘yan sanda, sojoji, NSCDC fiye da 250 zuwa gidan Sheikh Dutsen, lauyan ya ce sai ba a same shi ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya sa a kama fitaccen malamin Musulunci a Arewa? Gaskiya ta bayyana

Kamar yadda lauyan ya fada, ba a samu wani abin laifi da za a kama malamin da shi ba. Gwamnatin Bauchi ta nesanta kan ta daga lamarin.

Sheikh Dutsen Tanshi ya aiko sako

An ji Abdulaziz Dutsen Tanshi a gidan rediyon Freedom yana kira ga dalibansa su kwantar da hankalinsu a kan halin da ya shiga.

Malamin ya nuna masu cewa jarrabawa ce daga Ubangiji SWT kuma yana fatan zai ga bayanta, yake cewa ba sabon lamari ba ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel