Latest
Manjo Hamza Al-Mustapha ya koka kan matsalar tsaron Najeriya inda ya ce shugabannin da suka gabata ne suka lalata tsaron kasar da rashin yin katabus.
Tsohon Janar na sojoji, Garba Duba wanda ya fafata a juyin mulkin shekarar 1966, ya riga mu gidan gaskiya a yau Juma'a 18 ga watan Mayu a birnin Abuja.
Yayin da ƙimar Naira ke kara taɓarɓarewa a kasuwar musaya, jigon PDP ya gano cewa gwamnan CBN, Yemi Cardoso da ministan kuɗi, Wale Edun ne asalin matsalar.
Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta tabbatar da dakatar da mamba mai wakiltar Kaura Namoda da Birnin Magaji, Aminu Sani Jaji kan zargin cin amana.
Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan irin tsare-tsaren da ya ke kawowa inda ya ce za a amfana nan gaba.
Biyo bayan rikicin jam'iyyar APC, shugaban kasa ya kafa kwamitin da zai kawo wanda zai maye gurbin Ganduje. Sabon shugaban zai fito ne daga Arewa.
Gwamnatin jihar Filato ta ba masu sayar da shanu wa'adin mako biyu domin su tashi daga kasuwar Kara da ke Bukuru. Yan kasuwar sun koka kan matakin.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kwara ta cafke likita da kuma masu taimaka masa guda hudu kan zargin batar da mahaifa da kuma cibiyar jariri a jihar bayan haihuwarsa.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta cewa mutane 500 yan bindiga su ka sace a jihar Zamfara, inda ya bayyana cewa mutane 4 'yan bindigar su ka dauka.
Masu zafi
Samu kari