'Ka Auri Ƴar Zamani,' An ba Adam A Zango Shawarar yadda Zai Riƙe Sabuwar Amaryarsa

'Ka Auri Ƴar Zamani,' An ba Adam A Zango Shawarar yadda Zai Riƙe Sabuwar Amaryarsa

  • A ranar Lahadi, 17 ga Agusta 2025, aka daura auren jarumi Adam A. Zango da jaruma Maimuna Musa,watau a shirin Garwashi
  • Marubuciya, Uwa Aishatu Gidado ta taya su murna tare da yin nasiha, inda ta gargadi Maimuna kan tsoron Allah da girmama miji
  • Uwa Aishatu ta shawarci Zango ya rike amanar aure, ya rinka nuna kulawa ga amaryarsa, kuma wannan ya zama auren mutu-ka-raba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - A ranar Lahadi, 17 ga Agusta, 2025, kafofin sada zumunta suka cika da labarin sabon auren da fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango ya yi.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Adam A. Zango ya auri jaruma Maimuna Musa wacce aka fi sani da Salamatu a shirin Garwashi (fim mai dogon zango).

An roki Adam A Zango ya kula da sabuwar amaryarsa, jaruma Salamatu ta shirin Garwashi.
Hoton Adam. A Zango a wurin wani shagalin bikin aure, tare da jaruma Salamatu ta shirin Garwashi Hoto: Fauziyya D. Sulaiman
Asali: Facebook

An yi wa Adam A Zango da Maimuna nasiha

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Sarki mai martaba a Najeriya ya rasu yana mai shekaru 89

Saboda tarihin auratayya na jarumi Adam A Zango, fitacciyar marubuciya, kuma mai ba da shawara kan zamantakewa, Uwa Aishatu Gidado Idris ta yi wa Zango nasiha a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da farko, Uwa Aishatu ta fara taya Adam A Zango da amaryarsa Maimuna murnar shiga daga ciki, tare da rokon Allah ya albarkaci zamantakewarsu.

Bayan haka, Uwa Aishatu ta shiga ba jarumi da ma jarumar shawara kan yadda za su iya tafiyar da aurensu don ya dore na har abada.

A bangaren Maimuna, fitacciyar marubuciyar ta gargade ne a kan jin tsoron Allah, tana mai cewa:

"Amarya ki ji tsoron Allah, ban da butulci ko rashin girmamawa."

Yadda ake so Adam Zango ya rike amaryarsa

Ta ce akwai bukatar Adam A Zango ya san cewa ya auri yarinya danya jagab, wadda ake kira a zamanance da GenZ, watau'yan bana bakwai, don haka dole ne sai ya yi hakuri.

Kara karanta wannan

Daga Japan, Tinubu ya lula zuwa kasar Brazil, an fadi lokacin dawowarsa Najeriya

"Da yake GenZ ka aura, to Adam ka sani ta san hakkokinta kuma idan ka nuna mata tana da hakkokin nata kuma za ka kiyaye su kamar yadda Allah ya fadi, to ba ka da matsala. Ka kara bincikar littafan addini sosai.
"Zango ka sani, 'yan GenZ suna da yawan lura, musamman mata. Ba a son a bar musu sakonni ba tare da an mayar masu da amsa ba.
"Ka rika saya mata 'shawarma,' ba tuwo kawai ba, kiɗa da abinci su yi daidai wadaida. Ka tuna Genz ba ta da hakuri, ka yawan wasa, za ta iya toshe ka a shafukan sada zumunta ko da tana a gidanka na aure ne.
"Idan ta ce 'ka bar ni,' gaskiya tana nufin 'zo ka rungume ni' ne, saboda ba sa wasa da kulawa. Ka rika saka hotonta a shafukanta, idan ba haka ba, za ta saka a Tiktok cewa, maza munafukai ne."

Kara karanta wannan

Mamakon ruwan ya lalata gidaje, ya raba mutane sama da 600 da muhallansu a Yobe

- Uwa Aishatu Gidado Idris.

An shawarci Adam A Zango ya rike wannan auren mutu-ka-raba
Jarumin Kannywood, Adam A Zango zaune a cikin wani daki yana shakatawa. Hoto: Adam A. Zango
Asali: Facebook

An roki Zango ya rike aurensa da kyau

A yayin da ta gama jera wa jarumi Adam A Zango wadannan shawarwari na yadda zai rike matarsa, Uwa Aishatu ta kuma yi masa nasiha a kan rike amanar aure.

"Ka da ka mayar da aurenka fim mai zango shida. Wannan aure ya zama shi ne zangon karshe, na har abada. Ka rike addu'a da soyayya, domin GenZ tana bukatar WiFi da kulawa."

- Uwa Aishatu Gidado Idris.

Me mutane ke cewa kan auren?

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu daga cikin 'yan Najeriya game da auren Adam A Zango.

Ya'u Shareef Kaduna:

"Adam A. Zango mutumin kirki ne, mun yi aiki tare da shi ba sau daya ba, ba sau biyu kuma, kuma ba mu taba samunsa da cin zarafi ko kuntata wa wata jaruma ba.
"Shi ya sa idan suka gan shi za ka ji suna kiransa da Daddy, saboda yana rike girmansa, kuma ba shi da mugunta, don haka ina da yakinin zai rike Maimuna cikin mutunci da girmamawa."

Kara karanta wannan

Da gaske jarumi Ali Nuhu ya rasu? Shugaban NFC ya warware rudanin da aka samu

Najeeb Marubuci ya ce:

"Baba Adamu mutum ne, na ji dadi sosai da ya yi wannan auren, yanzu zai kara girma da daraja a idon duniya, muna masa fatan alheri.
"Kuma ya auri mace mai kamun kai, ko wajen daukar fim aka je za ka same ta tana girmama kowa, ba a hayaniya da ita. Allah ya ba su zaman lafiya."

Aisha, da aka fi sani da Uwar Gulma a shirin fim din 'Yan Makaranta, ta ce:

"Shi fa mutum ne mai shiga zuciya, yana da kirki, idan muka je wajen aiki, za ka ga yana haba haba da mutane, shi dai kowa nasa ne.
"Don Allah mutane su kyale Daddy ya huta haka, a yi masa addu'a, Allah ya ba su zama lafiya, ya kawo zuriya ta gari."

Karanta nasihohin marubuciyar a kasa:

Adam A Zango ya yi hatsarin mota

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu daga cikin jaruman Kannywood sun tsallake rijiya da baya bayan gamuwa da hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Biki bidiri: Adam A. Zango ya zama ango, ya auri fitacciyar jarumar Kannywood

Fitaccen jarumi Adam A. Zango na daga cikin wadanda suka tsira, tare da Kb Zango da wani da ake kira Oga Abdul, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Jarumi Abdul M Sherif shi tabbatar da haka inda ya wallafa sanarwa a Facebook, yana rokon addu’a, inda yake cewa lamarin ya zo da sauki sosai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.