Wata Sabuwa: Kotu Ta Daure Fitaccen Mawaki Hamisu Breaker Wata 5 a Gidan Yari

Wata Sabuwa: Kotu Ta Daure Fitaccen Mawaki Hamisu Breaker Wata 5 a Gidan Yari

  • Mai shari’a S.M Shuaibu ya yanke wa Hamisu Breaker hukuncin daurin watanni biyar a gidan yari bisa laifin cin zarafin Naira a Jigawa
  • EFCC ta gurfanar da Breaker tare da G-Fresh Al'Ameen bayan an gan su suna lika Naira yayin bukukuwa, kuma sun amsa laifuffukansu
  • Kotun ta yanke hukuncin zaman gidan yari ko kuma biyan tarar N200,000 ga kowannensu, yayin da EFCC ke ci gaba da yaki da lika kuɗi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Mai shari'a S.M Shuaibu na babbar kotun tarayya da ke Kano, ya yanke wa fitaccen mawakin Hausa, Hamisu Sa'id (Hamisu Breaker) hukuncin zaman gidan yari.

Babbar kotun tarayyar ta kama Hamisu Breaker da laifin cin zarafin takardar Naira, inda ta daure shi watanni biyar a gidan yari.

Babbar kotun tarayya a Kano ta yankewa Hamisu Breaker hukuncin daurin watanni 5 a gidan yari
Hamisu Breaker zai yi zaman gidan yari na watanni 5 ko biyan tarar N200,000. Hoto: Hamisu Breaker
Source: Instagram

EFCC ta gurfanar da Hamisu Breaker a kotu

Kara karanta wannan

Gwamnonin 1999 sun nemi Tinubu ya ajiye raba tallafi, ya samar da ayyuka ga matasa

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da Hamisu Breaker a kotun, inda ta tuhume shi da yin liƙin kuɗi yayin wani biki, inji rahoton BBC Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Likin kudi yayin wani shagalin biki wani babban laifi ne da hukumar EFCC ta sha alwashin sanya kafar wando daya da masu aikata shi.

An ce mawaki Hamisu Breaker ya gamu da fushin hukumar EFCC ne a lokacin da aka gan shi yana lika kudi 'yan N200 a wani biki da aka gudanar a Hadejia, jihar Jigawa.

A cewar wata sanarwa da EFCC ta fitar a shafinta na Facebook, Hamisu Breaker ya watsa 'yan N200 har suka kai N30,000.

Tuhumar da EFCC take yi wa Hamisu Breaker

Tuhumar da ake yiwa mawakin na cewa:

"Cewar kai Hamisu Sa'id Yusuf, a wajajen watan Nuwamba, 2024 a Hadejia da ke jihar Jigawa, yayin da kake rawa a wani taro, ka watsa takardar kudi har N30,000.
"Wadannan kudin da ka watsa ya sa ka aikata laifi wanda ya ci karo da sashe na 21(1) na dokar babban bankin Najeriya, 2007, kuma yake da hukuncin a karkashin sashen."

Kara karanta wannan

Kano: Kotun tarayya ta tunkuɗa ƙeyar ɗan TikTok, G Fresh zuwa gidan kaso

Sanarwar EFCC ta ce Hamisu Breaker ya fara zaman magarkama ne tun daga ranar da aka kama shi, kuma aka gurfanar da shi gaban kotu.

Hamisu Breaker ya amsa laifin wulakanta Naira a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano
EFCC ce ta gurfanar da fitaccen mawaki Hamisu Breaker kan wulakanta Naira. Hoto: Hamisu Breaker
Source: Twitter

Hukuncin da kotu ta yanke wa Breaker

Yayin da aka karantawa Hamisu Breaker tuhumar da ake yi masa, ya amsa ba tare da wata jayayya ba.

Bayan ya amsa laifinsa, shi ma Mai shari'ar bai wani bata lokaci ba ya yanke masa hukunci: Zaman gidan yari na watanni biyar ko biyan tarar N200,000.

Wannan sharadi na biyan tara ne za a ce ya ceci wannan fitattun mawakin Arewa, domin ana kyautata zaton zai iya biyan tarar, wanda zai hana shi zaman gidan yari na wata biyar.

Duk da hakan, kama shi da aka yi da kuma hukuncin da kotu ta yi, zai kara fito da sakon EFCC a fili, na cewar ba za ta dagawa kowa kafa ba idan ta kama shi yana cin zarafin Naira.

"Ba mu ji dadi ba" Abba Hassan

Legit Hausa ta ji ta tuntubi babban mai yi wa Hamisu Breaker kida, watau Kashifu Amjad domin jin ko mawakin ya samu damar biyan tarar da aka yi masa.

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya sun dimauce da aka kai musu hari da dare, an sace shanu

Sai dai Kashifun kida ya ce ba shi da masaniyar ko Breaker ya biya kudin tarar domin ba su yi magana ba, bai kuma san ya fito ko har yanzu yana gidan yari ba/

"Gaskiya bani da masaniya. Eh ban sani ba ko ya biya ko bai biya ba. Ban ganshi ba tun lokacin da abin ya faru."

- Kashifun kida.

Abba Hassan Gezawa, wani mai waka a cikin masana'antar Kannywood ya ce ba su ji dadin abin da ya faru da mawakin ba, kasancewarsa sananne a ciki da wajen Najeriya.

Abba ya ce:

"Ba mu dadin abin da ya faru ba, amma ka san ita kaddara ba a tsallake mata. Shi kansa da ya san hakan za ta faru da bai lika kudin ba, kai kila ko bikin ma da bai je ba.
"Domin shi mutunci ya fi komai, musamman shi da ya ke fitaccen mawaki ne, ba zai so wani abu ya taba masa mutuncinsa ba, domin hakan na iya shafar sana'arsa."

Kotu ta daure G-Fresh watanni 5

Legit Hausa ta rahoto cewa Mai shari'a S.M Shuaibu na babbar kotun tarayya da ke Kano, ya yanke wa fitaccen dan TikTok, G-Fresh Al-Ameen hukuncin daurin wata biyar.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, majalisa ta amince Tinubu ya kinkimo bashin Naira tiriliyan 32.2

EFCC ce ta gurfanar da G-Fresh Al'Ameen, bayan an ga bidiyonsa yana watsa kudi 'yan N1000 a bikin bude shagon wata fitacciyar 'yar TikTok, Rahama Sa'idu a Tarauni da ke Kano.

Bayan ya amsa laifinsa ba tare da wata jayayya ba, babbar kotun tarayyar ta iza keyar G-Fresh Al'Ameen zuwa gidan gyaran hali ko ya biya tara N200,000.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com